Real Madrid ta gamu da cikas yayin da Barcelona ta yi nasara
Sergio Araujo ya farke wa Las Palmas ana gab da tashi daga wasa yayin da Real Madrid ta kasa nasara karo na biyu a jere a gasar La Liga.
Marco Asensio ne ya fara ci wa Real Madrid wadda ta bakunci ‘yan Palma a minti na 33, amma Domínguez ya rama minti biyar tsakani.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 67 sai Benzema ya ci wa Real Madrid ta biyu.
Sai dai kuma wannan nasara ta Madrid ba ta yi karko ba, domin ana gab da tashi ne a minti na 85 sai Araujo ya farke kwallon, aka tashi 2-2.
Bayan wasan na mako na shida Real Madrid tana zaman ta daya a tebur da maki 14.
Barcelona wadda tun da farko ta dan dare matsayi na daya bayan da ta lallasa Sporting Gijon 5-0, ita ce ta biyu da maki 13, yayin da Atletico Bilbao wadda ta ci Sevilla 3-1 tana ta uku da maki 12.
A wasan na mako na shida Eibar ta ci Real Sociedad 2-0, ta zama ta shida a tebur da maki 10, yayin da bakin nata suka yi kasa zuwa mataki na 10 da maki 7.
The post Real Madrid ta gamu da cikas yayin da Barcelona ta yi nasara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
