Shugaban Boko Haram ya saki sabon bidiyo akan ‘yan matan Chibok
Dan jaridar nan na Najeriya wanda hukumar sojin Najeriya ta nema a kwanakin baya tare da wasu mutane biyu, Ahmed Salkida, ya bayyana cewar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, ya saki sabon bidiyo.
Salkida, yadai fadi hakane a shafinsa na Tweeta a ranar Lahadin nan 25 ga watan satumba. Yace bazai saki bidiyon ba saboda nemanshi da hukumar sojin Najeriya tayi masa saboda sakin bidiyoyin da yayi na kungiyar Boko Haram din a baya.
Ahmad Sarkida, dan jaridar da sojin Najeriya suka gayyata a kwanakin baya akan ‘yan Boko Haram
Haka kuma, bidiyon daya bayyana a You tube anga inda shugaban na Boko Haram yake magana akan ‘yan matan chibok.
Haka kuma, Shekau yayi magana yarda musulmai sukayi fama akan addinin nasu tun a karnin baya, inda yace, an tura wani mutum kasar Egypt domin ya koyo addini na musulunci.
Yace, wannan mutumin ya dawo da kur’ani, yace tun alokacin yace mutanen dake karanta wannan kuma suke bin duk wata doka dake cikin littafin, to babu shakka mutanen zasuyi karfi sosai.
Shugaban na Boko Haram yace, a taron sirrin da akayi tun a lokacin, an cusa wasu tsari domin a wargaza musulincin, inda aka hada da tsarin hada ilimin Boko da taimakawa dakuma jin kade kade da wake wake.
Acewar sa, a sakamakon wannan, yawancin musulmai sun bata akan hanyar addininmu su duka Waida sunan su masu ilimin Boko ne.
Idan aka tuna dai dan jaridar ya fadi a shafinsa na Tweeta a ranar Talata 20 ga watan Satumba cewar, ” ya karaya dayima gwamnatin Najeriya magana, bayan da hukumar sojin kasar ta nemesa ruwa a jallo. Duk da cewar gwamnatin tace bata fahimci yadda abun yake bane da kyau, amman rayuwarsa ta riga ta tsorata dasu”.
A ranar 14 ga watan Agustan shekarar 2016 ne, hukumar sojin Najeriya ta fidda sanarwar neman Salkida tare da wasu sauran mutane guda biyu ruwa a jallo, bayan daya saki wani bidiyon da aka turo mashi, inda yace ‘yan matan chibok sunan a raye da ransu, a inda wasu kuma suka mutu sanadiyar ruwan harsasai da sojin sama sukayi musu.
The post Shugaban Boko Haram ya saki sabon bidiyo akan ‘yan matan Chibok appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.