Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Октябрь
2016

Sai na hukunta duk wanda yayi rashawa – Buhari

0

– Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mutanen Najeriya a kasar Jamus inda yayi Magana da su

– Shugaba Buharin dai yayi alkawarin kwar da rashawa a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya alanta yakin d rashawa kuma yace sai gwamnatinsa ta hukunta duk wanda aka kama da kashi a gindi.

A yanzu haka, shugaba Buhari  na artabu ne a kungiyar lauyoyi akan damke Alkalai da hukumar DSS tayi wanda aka ce ya saba doka.

KU KARANTA: Buhari ya ziyarci babban hafsan soja a asibitin Berlin

Yayin da yake Magana a kasar Jamus da mutanen Najeriya mazauna kasar Jmaus, shugaba Buhari yace: “Idan kuka yi aiki kuma kuka samu kudi,zamu duba nawa zaku biya haraji, amma wai ku dauki kudin gwamnati ku gudu, ba zai yiwu ba.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata yi kyauta gay an Najeriya masu kokari.

Yace: “Muna kokari matuka domin karfafa ma’aikatun mu musamman bangaren ilimi. Idan aka ilimantar mutum, abin da zaka iya masa kenan saboda ya tsira daga tunani mara kyau. Mutanen Najeriya na goyon bayanmu akan yaki da rashawan da muke yi , tsaro da kuma tattalin arziki.

The post Sai na hukunta duk wanda yayi rashawa – Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *