Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Bam ya tashi a tashar mota a Borno

0

Wani Bam ya tashi a tashar mota Muna a da ke garin Maidugurin jihar Borno

Wani tashin Bam a Maidugurin jihar Barno

A cewar kafar yada labarai ta Sahara Reporters, Bam din ya tashi ne a wata tasha da ke cikin garin Maiduguri da ake kira tashar Muna.

Bam din ya tashi ne da misalin karfe 9 na daren Laraba 23 ga watan Nuwamba.

Babu da cikakkaken rahoton yadda abin da ya faru, da kuma bayanin rasa rayuka, ko wadanda suka jikkata a tashin bam din da ake kyuatata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka ta da shi ba.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta 

A wani labari kuma rundunar sojin Najeriya ta yi wata arangama da wasu mayakan Boko Haram a inda ta hallaka 7 da daga cikin ‘yan ta’addan

A wata sanarwa da Kakakin rundunar sojin Kanar Sani Usman Kuka sheka ya sa hannu ta ce, sojoji na ta Bataliya ta 119 a karkashin dibishin na 8  da ke kauyen Kangarwa ne suka fafata da a ‘yan ta’addan a inda sojin suka hallaka su, wasu kuma suka tsere da raunuka.

Sanarwar ta ce, an jikkata sojoji 5 an kuma kai su asibiti a inda suke karbar magani.

Haka nan kuma a ranar Talata wasu rahotanni na cewa, ’yan ta’addan sun kai wani hari kauyen Dasa a inda sojojin suka fatattake su.

The post Bam ya tashi a tashar mota a Borno appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *