CHANJI! Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 mako mai zuwa
– Komai na tafiya dai-dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 mako mai zuwa
– Ranar da aka shirya gabatarwa shine ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba
– Shugaban majalisar dattawa na yan tsiraru, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan
Wani rahoto daga jaridar Thisday ya bayyana cewa akwai yihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 a ranar Alhamis, 1 ga watan Nuwamba a gaban majalisar dokoki.
Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 mako mai zuwa
Shugaban majalisar dattawa nay an tsiraru, sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana wannan, a karshen mahawara a kan 2017-2019 Medium Term Expenditure Framework (MTEF) da kuma Fiscal Strategy Paper (FSP) a jiya, 23 ga watan Nuwamba.
Akpabio yayi wannan sanarwan ne a lokacin da yake maida martani ga soka daga sanatoci na cewa a dawo da takardun gay an majalisa.
KU KARANTA KUMA: Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama ya fadi a Makurdi
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom yace yin haka zai taimaka gurin duba a cikin shirin gabatar da kasafin kudin 2017 a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba.
Akpabio ya bukaci abokan aikinsa da su aika da takarda ga kwamitin da ya dace sannan kuma subar kwamitin tare da alhakin maganta aibin.
A halin yanzu, wani rahoto daga mujallar Economic Confidential ya kawo cikakken bayani kan yadda ministoci biyu a majalisar shugaban kasa Buhari ke wuyan juna kan kasafin kudin 2016 da 2017.
Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita @naijcomhausa
The post CHANJI! Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2017 mako mai zuwa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.