Wani Bahaushe ya kafa tarihi a kasar Amurka (Karanta)
– An zabi wani musulmi Bahaushe dan asalin kasar Ghana a matsayin kansila a majalisar karamar hukumar birnin Portland Maine da ke jihar Maine ta Amurka
– Zaben nasa na zuwa ne yayinda Musulmi da sauran baki a Amurkar ke ci gaba da nuna fargaba game da makomarsu a kasar bayan zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasa; saboda matakan da ya ce zai dauka na ko dai kora, ko na hana wasu shiga kasar
A cikin wata hira da majiyar mu, sabon kansilan Pious Ali ya ce aikin da ya yi na baya a hukumar ilmi ta karamar hukumar ne ya taimaka wajen zabensa.
(An zabe ni ne) domin mutane sun ga aikin da nake yi. Sun ga aiki na aiki ne na taimakon yara. Shi ya sa kowa na son mai taimakon yara.”
KU KARANTA: Jam’iyyun adawa 16 sun goyi bayan PDP a Jihar Ondo
A kwanan baya ma dai wata ‘yar asalin Somalia kuma ‘yar gudun hijira ta kafa tarihi a Amurka, inda ta zama ‘yar majalisar wakilan kasar.
Ta shai da wa majiyar mu cewa yaki da tsangwamar musulmai bakar fata da ake yi a Amurkar na daga cikin abubuwan da zata fi bai wa fifiko. An dai zabi Ilhan Omar mai shekaru 34, don ta wakilci jihar Minnesota a majasalisar wakilai.
Kuma ta shaida wa Bola Munsoro ta sashen turanci abubuwan da take so ta cimma a matsayin ta na wakiliyar al’uma. Ita dai Ilham ta na da shekaru 12 suka isa Amurka ita da iyayen ta a matsayin ‘yan gudun hijira, kuma ta fara makaranta ne daga aji shida na firamare.
Ta dai sha fuskantar tsangwama a wajen ‘yan uwanta dalibai, saboda rashin iya turancin ingilishi.
Amma idan ta yi wa mahaifin ta korafi, ya kan bata kwarin gwiwa da cewa ta dage da karatu, matukar iya harshen ingilishi to za ta samu sassaucin tsangwama daga abokanta.
Burin Ilham dai a yanzu bai wuce ganin ci gaban ‘yan uwanta ‘yan gudun hijira da suke zaune a Amurka shekara da shekaru.
The post Wani Bahaushe ya kafa tarihi a kasar Amurka (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.