‘Yan Najeriya sun kira Obasanjo Munafuki
– Cif Olusegun Obasanjo ya zargi wasu daga cikin tsare-tsaren Gwamnatin Kasar nan
– Wani tsohon shugaban kasa ya kira Shugaba Buhari da ya daina tuna baya, ya tsaya yayi aiki da kuma sai dai mutanen Najeriya sun ce Obasanjo munafuki ne
‘Yan Najeriya ba suyi wa tsohon shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo rangwame ba, bayan da ya soki tsarin gwamnatin Shugaba Buhari da ma na Goodluck Jonathan. Jaridar Premium Times ta rahoto wata takarda da Obasanjo ya gabatar jiya a Garin Legas inda ya soki Gwamnatin Tarayya.
Mutanen Kasar dai sun ce irin su Obasanjo ne suka kashe Najeriya ba wasu ba, don haka su rufe baki. Mithras Love yake cewa, ‘Allah ya kara. Ba shi bane yake murna Jonathan ya fadi. Yayi masa kyau ai.
KU KARANTA: Shugabannin PDP suka kashe mu-Neja-‘Yan Delta
Wani kuma mai suna Kelvin Ahamefula cewa yayi: ‘Duk laifin su Shugaba Obasanjo ne ta sa muke cikin irin wannan yanayi. Ai ya kuma san tun can Shugaba Buhari ba zai iya ba…Hakanan ya matsa aka kora Jonathan.’
Shi kuwa Fride Chikwuemeka da kakkausan harshe yace: ‘Ya rasa ko meyasa mutane ke kula wannan goggon. Ai a asara ne a tsaya kula wannan rikitaccen’, inji Chikwuemeka.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post ‘Yan Najeriya sun kira Obasanjo Munafuki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.
