Abubuwa 5 da Obasanjo ya fada game da gwamnatin su Buhari
– Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi wasu tsare-tsaren kasar nan
– Wannan karo Cif Obasanjo ya zo wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da zafi
– Haka nan tsohon shugaban kasar yayi kaca-kaca da tsohin shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya gabatar da wata kasida jiya, a Legas, inda yayi kaca-kaca da wasu tsare-tsare na Kasar nan. Jaridar Premium Times ce dai ta rahoto wannan labari. Mu kuma mun kawo maku muhimman abubuwa daga cikin abin da ya fada:
KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi raddi ga Buba Galadima
- Babban ciwon kan kasar nan itace Majalisa. Ko da an gyara Bangaren shari’a, ya za ayi da ‘Yan Majalisa, wanda sun fi kowa rubuewa?
- Duk duniya babu inda ake da ‘yan majalisa irin na Najeriya. Albashin kowane Sanata ko dan majalisar Tarayya ya haura Miliyan goma a kowane wata. Dole a hukunta wadanda suka yi badakalar kasafin kudi.
- Rashawa ta shiga har gidan Soji, Sojojin Kasar sun koma sata cikin ‘yan shekarun bayan nan. Ta yaya Janar na Soja zai saci kudin sayen makamai.
- Bai dace Shugaba Buhari ya karbo bashin Biliyan $30 ba
- Gwamnati ta rika jawabi a kai-a kai ga ‘Yan Kasa a irin su Rediyo da Talabijin
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Abubuwa 5 da Obasanjo ya fada game da gwamnatin su Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.
