Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim ya ragargaji Fani Kayode
– Dan takarar gwamna a daya bangaren jam’iyyar PDP a zaben jihar Ondo Jimoh Ibrahim, ya mayarwa da Femi Fani Kayode martani bisa wasu kalamai ya yi game da takararsa
– Femi Fani Kayode ya zargi Jimoh Ibrahim da neman satar takarar gwamnan jam’iyyar PDP ta bayan gida
Femi Fani-Kayode bakinsa ba ya haila a harkar siyasa
Hamshakin attajiri Jimoh Ibrahim ya mayarwa da Femi Fani-Kayode martani dangane da wasu kalaman da yayi kan takarar da yake yi a matsayin gwamna a daya bangaren jam’iyyar PDP karkashin Ali Modu Shariff.
Dan kasuwan da ya koma harkar a siyasa, a wasu sakwanni da saka a shafinsa na Tuwita, ya ce, yana mai alfaharin cewa shi attajiri ne da ya kai matsayin Biloniya, kuma ba a taba zargin mahaifinsa da cin amanar kasa ba, kuma bai taba auri-saki ba, ko kuwa mace sama da daya ba, kuma duk da tarin dukiyarsa bai taba zaman fursuna a gidan yari na Kuje ba.
A sakon na Tuwita Jimoh Ibrahim ya kuma kira Fani Kayode wanda ba shi da alkibla a rayuwa,“…mutumin da zai iya yi maka waka da kida da kuma rawar mokosa idan har za ka ba shi tuwo.”
A wani sakon kuma yana mai cewa, “idan ka ga wanda ya san Femi Fani-Kayode, ga sako zuwa gare gare shi, NI BILONIYA NE KUMA BA NA SHARI’A DA EFCC.”
Attajirin dan siyasa kuma mai lambar yabo na OFR, a wani sakon yana mai cewa ga Fani Kayoden,“ kafin shekara 2019 zan taimaka in samo kwararrun masana kimiyya na duniya da za su yi maka magani cutar da ke damunka a kwakwalwa.”
KU KARANTA KUMA: An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP
Tun farko dai, a wasu jerin sakwanni ta dandallin sada zumunta da muhawara a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, Femi Fani-Kayode ya caccaki dan siyasan, a inda ya kira shi da ma handami, mai kokakarin kwace takarar gwamnan jihar Ondo a ta bayan gida.
Femi Fani Kayode tsohon Ministan sufurin jiragen sama ne a zamanin mulkin Obasanjo, kuma jigo ne a jam’iyyar PDP, ya kuma taka muhimmiyar rawa a babban zaben shekarar 2015 da jam’iyyar ta sha kaye.
Ku biyomu a Tuwita a @naijcomhausa
The post Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim ya ragargaji Fani Kayode appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.