Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim bai saduda ba
– Dan takarar zaben gwamna a jihar Ondo a karkashin daya bangaren jami’yyar PDP, Jimoh Ibahim ya mayar da martani ga kayen da ya sha a kotun koli na soke takararsa
– Jimoh Ibrahim ya yi watsi da hukuncin kotun koli, ya kuma gayyaci magoya bayansa zuwa shagalin bikin cin zabensa a ranar Lahadi 24 ga wata bayan kada kuri’a
Jam’iyya daya ‘yan takara biyu: Ibrahim da Jegede a zaben gwamnan jihar Ogun
A yau 24 ga watan Nuwamba ne Kotun koli ta yi watsi da bukatar da attajirin dan siyasar nan ya yi na daukaka kararsa daga kotun daukaka kara, kan abokin karawarsa na daya bangaren jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede.
Sai dai rahotanni na cewa, hamshakin attajirin da ya koma siyasa bai yarda da hukuncin kotun kolin ba, ta irin sakonnin da ya ke ta aikawa a dandalin sada zumunta da muharawa na Tuwita a inda yake mika goron gayyata zuwa shagalin bikin cin sa zaben ranar Lahadi, bayan kammala kada kuri’a
A wani kwarya-kwaryar zama da alkalan kotun kolin su biyar suka yi a karkashin jagorancin mai rikon mukamin babban mai shari’a na kasa Walter Onnoghen, bayan sauraron bukatar mai shigar da kara, bisa dagewar mai shigar da karar ta hannnun lauyansa Barister Nwofor. Ta yanke hukuncin watsi da bukatar ta sa.
KU KARANTA KUMA: An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP
Bisa wannan hukuncin attajirin dan kasuwan ba shi ba takara a zaben gwamnan jihar Ondo a karshen makon nan.
Attajiri Jimoh Ibrahim na neman kotu ta halasta masa takarar da ya ke yi a matsayin gwamnan a zaben a jihar Ondo a karkashin bangaren jam’iyyar PDP, ta kuma haramtawa Eyitayo Jegede daga daya bangaren na PDP yin ikirari, da kuma daukar kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Rashin samun nasararsa ga wannan bukata a kotun daukaka kara ne ya sa ya garzaya kotun koli tare da dagewar da kuma matsa lambar lauyoyinsa na a sauraresu, an kuma yi hakan, ga kuma hukuncin da ta yanke.
Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa
The post Zaben Ondo: Jimoh Ibrahim bai saduda ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.