Jibril ya kalubalanci APC kan yunkurin cire Timi Frank
Shugaban cin jam’iyar APC ya samu mummunan suka daga dan majalisar tarayya na Kano Jibril Abdulmumin wanda ya kalubalance su da yunkurin cire mataimakin mai watsa labarai na jam’iyar Timi Frank.
Jibril wanda mamba ne a majalisar wakilai a birnin tarayya mai wakiltar mazabar Kuru da Bebeji na jahar Kano, ya rubuta a shafin tuitar shi ranar 24 ga watan Nuwamba cewa” lalle wannan rashin adalci ne ga jam’iyar in har tana tunanin cire Timi Frank daga matsayin shi bayan danne mai hakkin shi da aka yi na tsawon lokaci.
Kamar yadda ya bayyana yace” matakain da jam’iya ta dauka karkashin jagoran cin Oyegun John Odigie rashin adalci ne kuma be dace ba.
KU KARANTA: Obasanjo ya goyi bayan salon mulkin Buhari na tsaftace fannin shari’a.
Jibril wanda ba dadewa shugabanin majalisa suka dakatar da shi a majalisa kan tona asiri da yayi kan almundahana da akayi a cikin kassafin kasa watanni 4 da suka gabata, ya zama Sanannen kan hana cin hanci da gaskiyar shi.
Duk da cewa jibril ba wani babban dan jam’iyar bane, amma abun da yake zargi ze iya bata jam’iyar ga idon duniya duk da rikici da yake damun jam’iyar.
Naij.com zata iya tuna maku cewa an hada wani kwamiti a kudu maso kudu na yayan jam’iyar inda aka kama Frank Timi yana yi ma wata jam’iya aiki, bayan zargin da yayi tayi a fili cewa Odigie-Oyegun ya kasa dai dai ta jam’iyar kan rikicin da ke damun ta.
Frank yana goyon bayan Bola Tinubu kan Odigie-Oyegun ya sauka kan makamin sa, kira kuma da yayi na cewa a maida Frank Timi a matsayin shugaban watsa labarai na jam’iyar dan fara shiri tun kafin tafiyar Lai Muhammad , wanda a yanzu yake matsayin minista.
Ku bi mu a shafin mu na Tuita: @naijcomhausa
The post Jibril ya kalubalanci APC kan yunkurin cire Timi Frank appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.