Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Ноябрь
2016

Kungiyar kare hakkin biladama ta zargi Nigeria da kisan mutane 150 (Karanta)

0

– Kungiyar kare hakki bil’adama ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Nigeria da kisan akalla masu zanga-zangar lumana150 a watan Agustan bara

– Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan makamai wajen murkushe masu zanga-zangar da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar

Rundunar Sojan dai ta musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron kasa.

Yunkurin kafa kasar ta Biafra ne dai ya haddasa yakin basasa a kasar kusan shekaru 50 da suka wuce.

KU KARANTA: Najeriya ta daukewa Dangote biyan haraji

A wani labarin kuma, jiya ne Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya ce jami’ansa 128 ne suka mutu sakamakon hare-haren da masu tsattsauran ra’ayi suka kai musu a bakin-aikinsu.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar DCP Don N Awunah ya aike wa manema labarai ta ce an kashe jami’an ‘yan sandan ne a sassa daban-daban cikin wata uku.

Sanarwar ta ambato Babban Sufeton ‘yan sandan Ibrahim K. Idris yana bayyana hakan a matsayin wani abu “mai matukar tayar da hankali”.

Ya kara da cewa “wani abin takacin kuma shi ne yadda ake rusa ofisoshin ‘yan sanda da kaddarorin mutane.

Sanarwar ta bayyana cewa a kwanakin baya an kashe ‘yan sanda a kauyen Dankamoji na karamar hukumar Maradu da ke jihar Zamfara, da garin Abagana da ke Anambra da kuma Okrika da ke Ribas.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin yin bakin kokarinta domin kula da iyalan jami’anta da aka kashe.

Ta yi kira ga ‘yan kasar na gari su taimaka wa ‘yan sanda idan suka gan su a irin wannan hali.

The post Kungiyar kare hakkin biladama ta zargi Nigeria da kisan mutane 150 (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *