Wajibi ne a binciki Obasanjo akan badakalar $16billion- SERAP
– An ambaci sunan Olusegun Obasanjo a cikin badakalar $16billion
– Kungiyar fafutuka ta Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) tayi kira a bincike tsohon shugaban kasa Obasanjo
– SERAP tace anyi mahaukacin rashawa lokacin gwamnatin Obasanjo
Kungiyar yaki da rashawa tayi kiraga alkalin alkalai Justice Water Samuel Nkanu Onnoghen, da ya bada umurni a bincike badakalar kudin wutan lantarki karkashin gwamnatin Obasanjo.
Ana tuhumar gwamnatin Obasanjo da laifin rib da ciki da kudin kwangilan wutan lantarki $16billion.
KU KARANTA: An kubuto da mutane sama da 40 daga hannun yan bindiga
SERAP ta bayyana hakan ne cikin wata wasika da ta aika ma Alkalin alkalai a ranan 24 ga watan Nuwamba inda babban lauyan kungiyar ya sanya hannu.
Game da cewar Jaridar Sahara Reporters, Serap ta tuno zaman majalisan wakilai da akayi akan badakalar kudin wuta tsakanin shekarar 1999 da 2007 , ta shaidu da hujjoji da aka samu wanda ke nuna yadda wasu yan tsiraru suka hadiye kudin.
Wani mai shaida wanda ya bada shaida yace an kaddamar da aikin a Gembu , kilomita 25 zuwa Mambilla Amma basu taba zuwa mambillan ba.
Kana kungiyar ta bayyana ma Alkalin alkalai cewa an bayar da kwangila domin gina tashan wuta Kainji, Egbin, Afam da Ugehlli amma baá gudanar da aikin ba duk da cewa an sanya cikin kasafin kudin kamfanin wuta a tsakanin shekarar 199 zuwa 2007.
Kudin wadannan kwangila ya kai $142million.
Ku biyo mu a shafin sada zumunta a Tuwita @naijcomhausa
The post Wajibi ne a binciki Obasanjo akan badakalar $16billion- SERAP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.