Gobara ta kama ma’aikatan Shari’a a Jihar Kaduna
– Gobara ta kama ma’aikatan shari’a a Jihar Kaduna da safiyar yau
– Sama da dakuna 12 da dafturan aiki ne akayi hasara
Ma’aikata Shari’ar Jihar Kaduna ta kama da gobara a yau litinin 20 ga watan yuni , gobarar ta fara ne misalin karfe 2 na dare , Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa anyi hasaran dafturan gwamnati masu amfani da dama .
Sama da dakuna 12 da ke gidan saman ma’aikatan ne suka kone kurmus, daya daga cikin dakunan da gobarar ta shafa ofishin babban lauyan Jihar Kaduna.anyi hasaran kayan aiki da dama da ke cikin dakuna 12 da suka kone, wadanda sun kunshi abubuwa masu muhimmanci da suka shafi gwamnatin Jihar.
Game da wata majiya a ma’aikatan, hukumar kashe wutar gobara wato fire briged sun zo wurin da gaggawa kuma suka kashe wutan, hakan ya sa gobarar ba ta shafi sauran dakunan ba ,da kuma sauran ma’aikatar da ke kusa da ma’aikatar Shari’a.
“Hukumar faya briged sun zo wuri sun kasha wutan. Idan ba haka ba da sauran dakunan da kuma sauran ma’aikatar da ke kusa da ma’aikatar shar’iar sun kama” Majiyar ta ce.
KU KARANTA: Abin da ya kawo matsalar wuta-Fashola
Har yanzu, ba’a san abun da ya jawo gobarar ba, saboda ba ma’aikacin ma’aikatar da son yi wa manema labarai Magana, sun ce gwamnatin Jihar Kaduna bata yarda su yi Magana ba, amma gwamnatin ta ranstar da bincike domin sanin abinda ya jawo gobarar, har yanzu dai ,ba mu da labarin rasa rayuka ko jin rauni.
The post Gobara ta kama ma’aikatan Shari’a a Jihar Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.