Kungiyar matasan Ohaneze koko Ohaneze Youth Council (OYC) ta nisanta kanta daga matsalolin dake damun kungiyar ‘yan rajin Biafra ko Indigenous People Of Biafra (IPOB) wadanda suka jaza rabuwar kungiyar gida biyu.
Wani gungu mai kiran kansa gyararrun ‘yan rajin Biafra koko Reformed Indigenous People Of Biafra (TRIPOB) ya balle daga IPOB wanda yace ya daina gwagwarmayar neman ‘yancin kasar Biafra, mamadin haka suna bukatar ganin ana damawa da Igbo a Najeriya. Ana cewa Ohaneze nada hannu wajen kirkirowar sabon gungun amma Vanguard ta ruwaito OYC na cewa ba hannun kungiyar ko shugabanta Mazi Okechukwu Isiguzoro cikin rikice rikicen kungiyar ‘yan Biafran.
“Wannan karya ce karara. Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo a duk duniya baki daya bata da wata alaka da TRIPOB kuma bata da hannu cikin rigingimun dake addabar IPOB. Mun yima wani wai shi Elliot Uko tare da mai magana da yawun IPOB Clifford Iroanya gargadi da su daina cin dunun shuwagabannin matasan Ohanaeze Ndigbo ko kuma mu dauke su tamkar abokan gaban Igbo.
Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo a duniya baki daya itace babbar kungiyar matasan Igbo kuma bata goyon bayan kirkiro Biafra kuma bata goyon bayan shugaba Buhari a ranar 1 ga Oktoba 2016, amma tana goyon bayan sakin duk ‘yan Biafra dake tsare.
“Mun amince a sake fasalin kasar kamar yadda taron kasa da akayi cikin 2014 ya zartas kuma muna kiran shugaba Buhari da ya duba. Muna ba IPOB shawara su daina tsoma kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo cikin parpagandarsu” cewar Mazi Okemiri Alex a wata takarda daya sama hannu, a matsayin shugaban shuwagabannin Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo.
В депо «Вязьма» отметили профессиональный праздник соревнованиями по лазертагу
Велоспорт для всех: начни вместе с ENERGY
«Детям полезно принимать участие в любой движухе, связанной с творчеством, музыкой и спортом!» В Москве завершился Международный фест-форум «Голоса Мира» 2025
Профессиональные бои состоятся в Нижнем Новгороде 9 августа
Аномальная жара: До +41 °С в Чечне и Ингушетии, +30 °С в Карелии и Архангельске
Алтайский край оказался одним из антилидеров по качеству автодорог
Коми, Камчатку, Архангельскую, Иркутскую, Калужскую, Костромскую, Курскую, Свердловскую и Оренбургскую области эксперты отнесли к регионам, где на осенних выборах "протестный потенциал выше среднего", говорится в докладе...
Амурская область оказалась в числе аутсайдеров по качеству дорог