Kawunan tsagerun Neja Delta sun rarraba saboda wannan dalilin (Karanta)
– ‘Yan bindigan Neja Delta sun yawaita hare-haren da suke kaiwa kan kamfunan man fetur a yankinsu tun bayan da dattawansu suka gana da shugaban Najeriya Muhammad Buhari
– Shugaban Najeriya yayi taron tattaunawan ne da nufin shawo kan riginrimun da mayakan suka jefa yankin Niger Delta ciki har ma sun shafi hakar man fetur
To saidai maimakon hare-haren su ragu bayan ganawar da dattawansu sai gashi kwatsam karuwa ma su keyi. Kamfanonin mai da yawa ne yanzu mayakan suka kai ma hari tare da yi masu barna matuka.
KU KARANTA: Shugaban kasa ya kori ministan bunkasa tattalin arzukinsa
An samu rarrabuwar kawuna da kungiyoyin dake tada kayar bayan inda kowannensu ya sha gaban kansa ba tare da yin la’akari da komi ba. Kowace kabila nada nata muradun haka ma dattawan yankin da yanzu an gani a fili cewa basu da wata martaba a idanun mayakan.
Da wuya a samu wata masalaha idan ba’a samu wakilai daga kowane bangare ba. Harin baya bayan nan da tsagerun suka kai ya dada firgita jama’a saboda ya kawo cikas a harkokin hakko danyan mai a yankin. Mayakan sun fasa bututun mai masu mahimmanci dake aika danyen mai zuwa kasashen waje na kamfanoni guda uku.
Wani dattijon yankin yace suna cikin wata irin rayuwa ce inda babu wanda yake ganin girman kowa saboda haka ana tababan irin mutunci da dattawan ke dashi a idanun mayakan.
A wani labarin kuma, A Najeriya, wasu kungiyoyin matasa sun rufe kofar shiga majalisar dokokin kasar, suna cewa ba za su gusa ba sai ‘yan majalisar sun sauya halayensu, sun bi sahu a yakin da gwamnatin kasar ke yi da cin hanci da rashawa. Matasan dai na zargin cewa babu abin da ‘yan Majalisar suka sa a gaba face son zuciya, lamarin da suka ce ba zai haifar wa Najeriya alheri ba.
Matasan, wadanda suka yi gangami a mashigar Majalisar dokokin Najeriyar sun ce sun dauki wannan matakin ne don nuna goyon bayansu ga aniyar shugaba Buhari, ta yaki da cin hanci da rashawa, yakin da suka ce wajibi dukkan masu kishin kasar su shiga tafiyar.
A cewarsu sai da suka tsaya suka yi nazarin dabi’un ‘yan Majalisar dokokin Najeriya, kafin su kai ga zanga-zangar tasu ta zaman dirshan, amma sun fahimci cewa, kamar yadda suke zargi ba kishin kasa ba ne a gaban ‘yan Majalisar.
The post Kawunan tsagerun Neja Delta sun rarraba saboda wannan dalilin (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.