Sojoji sun kashe Yan Boko Haram 16 a Pulka
– Sojojin Najeriya sunyi arangama da yan Boko Haram a Pulka
– Yan Boko Haram sun fara wuraren sojoji guda 3 hari a safiyar 8 ga watan Maris
– An kashe yan Boko Haram 16, an kama 1 da rai, an kwace makamai
Mota kirar Hilux da aka amshe daga hannun yan ta’addan
Rahotanni na nuna cewa rundunar sojoji daga Task Force Birigade na 26 da 28 a safiyar Talata sun hana Yan Boko Haram farma garin Bita da Pulka hari. Sojojin kuma sun kashe yan kungiyar Boko Haram guda 16 a lokacin da suke tserewa kusa da dajin Sambisa. An kuma kama guda 1 da rai.
Jaridar Dailypost ma ta ruwaito cewa rundunar Task Force na 114 suma yan Boko Haram sun kai masu hari inda suka taho ta hanyar Damboa, Tokumbere da Pulka.
Jami’i mai hudda da jama na sojin kasa ya bayyana cewa ” Daga karshe, mun kashe yan Boko Haram 2, mun kama 1 da rai wasu dayawa kuma sun samu raunuka. Abunda ya samu wadanda suka kaima Pulka hari ma yafi wannan.
” Sojojin wadanda a shirye suke sun hana su farma garin sannan kuma duka 16 da suka kai harin an kashe su. Kuma an amshe makaman su bindigar AK-47 guda 11, GPMGs guda 3BGM guda 1, motar Hilux da kuma harsashi mai yawa.
” Sojojin mu kuma babu wanda ya mutu sai dai guda 3 da suka samu rauni kadan.
Sojojin Najeriya na cigaba da samun nasara akan yan kungiyar ta Boko Haram
The post Sojoji sun kashe Yan Boko Haram 16 a Pulka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.