Yan sanda sun sanya dokar ta baci a kaduna
– Yan sandan jihar Kaduna sun sanya dokar ta baci a jihar kaduna
– Sun sanya dokar ne saboda satar mutane datayi yawa a jihar Kaduna
– Jami’i mai hudda da jama’a na jihar ya musanta zancen
Yan sandan Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa dokar ta baci da aka sanya a jihar Kaduna an sanya tane saboda umurnin shugaban yan sandan najeriya, Solomon Arase.
Rundunar yan sandan Najeriya ta jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a jihar saboda satar mutane data yawaita a cikin jihar.
DSP Zubairu Abubakar, jami’i mai hudda da jama’a na jihar Kaduna ne ya bayyana haka a yau 5 ga watan Afrillu.
Ya bayyana cewa kafa dokar ta bacin umurni ne daga shugaban yan sandan Najeriya, Solomon Arase.
Abubakar ya bayyana cewa an kafa wata rundunar hana garkuwa da mutane ta musamman domin ganowa da kuma kokar masu aikata lafin a cikin jihar Kaduna.
Wakilin Naij.com ya bayyana cewa babu wani alamun dokar ta baci a cikin jihar. Da aka nemi jami’i mai hudda da jama’a na jihar ya maganata sai yace ba’a saurare da kyau ba.
A wattani baya da suka wuce, mutane da yawa an sace su inda ake neman kudi domin a saki wadanda aka sace din.
Mansur Ahmad, wanda ya kasance Daraktan a NNPC amma yanzu yana aiki da Dangote bai jima da aka sake shi ba.
Idan za’a iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kara yawan yan sanda dubu Goma a Najeriya. Shugaban kasan yayi wannan alkawari ne tun a lokacin da aka rantsar dashi a watan Mayun 2015.
A wani labarin kuma, shugaban kasa yayi alkawarin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya da kuma hukunta dukkanin masu kokarin tada zanne tsaye a fadin Najeriya.
Sojojin Najeriya dai na ciga ada samun nasarori akan kungiyar Boko Haram inda suke kama wasu suna kashe wasu daga cikin manya manyan kwamandojin kungiyar.
The post Yan sanda sun sanya dokar ta baci a kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.