Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 11,595
– Kanar Sani Usman ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun kubutar da mutane daga matsugunin Boko Haram daban daban
– Ya bayyana cewa sojojin zasu kula da hakkin bil adama a lokacin yakin
Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane sama da 11,595 daga wajen yan kungiyar Boko Haram a wannan watan. Sun kubutar dasu ne akan cigaba da daikila kungiyar da akeyi a Arewa maso gabashin najeriya.
Inda ya bayyana haka a wata takardar manema labarai daya aiko ma naij.con. ya bayyana cewa an kubutar dasu ne daga alkaryu daban daban wadabda yan kungiyar suke fakewa kafin sojojin Najeriya su shiga ciki.
” A ranar 1 ga watan Maris na 2016, rundunar Task Force ta 155 ta amshi mutane 10,000 yan gudun hijira daga daga kasar Kamaru a yankunan Banki da Bama. Sannan kuma rundunar sojoji na musamman (AHQ SF) sun kubutar da mutane 63 daga maleri. Sannan kuma rundunar ta sake kubutar da mutane 779 daga yankin Fotokol dake iyakar Najeriya da kasar kamaru.
” A makon farko na watan Maris na 2016, rundunar Task Force ta 254 ta kubutar da mutane 45 daga Kuaguru, sannan runduna ta 143 ta kubutar da mutane 27 a Gadayamo, 15 a Galadadani Madagali da kuma 10 daga kauyen Disa.
Kanar Usman ya bayyana cewa duka mutane da aka kubutar yawan su yakai 11595 tun daga farkon watan Maris na 2016. Ya kuma bayyana cewa sojojin najeriya na nan kan bakan su na kawo zaman lafiya a Najeriya da kauda kungiyar Boko harm.
Idan za’a iya tunawa, a shekarar data wuce shugaban kasa Muhammadu Buhari yaba sojojin Najeriya wa’adi dasu kawo karshen kungiyar Boko Harm zuwa watan Disamba daya wuce. SOjojin sun cinma nasarori sosai inda suka kakkabe yan kungiyar daga garuruwa da kuma matsugunin da suke zaune a gurare daban daban.
A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ana bukatar Dala Biliyan 9 domi gyara yankin Arewa maso gabas wanda Boko haram ta lalata a cikin shekaru 4. Mai taimaka mataimakin shugaban kasa akan hudda da jama’a, Laolu kande ne ya bayyana haka inda suka fidda rahotan binciken wanda aka gudanar a yainkin na Arewa maso Gabashin na Najeriya.
The post Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 11,595 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.