Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata 5 ga watan Maris. Ku duba domin ku same su.
Manyan labarai na ranar Talata
1. Shugaban Majlisar Dattawa ya koma kotu
Bukola Saraki ya sake komawa kotu akan tugumar kin bayyana kaddarorin shi da hukumar CCB take yi mashi.
2. Boko Haram ta kashe mutane 20,000 a shekara 4 – Fadar Shugaban kasa
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta kashe kimanin mutane 20,000 tunda ta fara ta’addanci. Cikin manyan asarorin da ta haddasa ke nan.
3. Hukumar yan sanda ta sanya dokar ta baci a Kaduna
Hukumar yan sandan najeriya ta sanya dokar ta baci a jihar Kaduna saboda garkuwa da mutane da akyi a jihar musamman manyan birane. Sun bayyana cewa dokar daga Sifeto janar na yan sanda take
4. Alkali na san kai – Lauyan Nnamdi Kanu
Ifeanyi Ejifor, Lauyan Nnamdi Kanu, ya bayyana cewa Alkalin dake yima Nnamdi Kanu Shari’a yana san kai. Lauyan ya bayyana haka ne a jiya
5. Elrufai yayi gargadi akan sabuwar kungiyar ta’addanci
Gwamna Elrufai ya bayyana cewa sanya dokar wa’azi tana da nasaba da dakila sabuwar kungiyar mai bullowa. Ya bayyana cewa dokar ta zama wajibi ne a yanzu
6. Shiryawar karya mukayi da Fayose – Temitope
Tsohon Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Ekiti ya bayyana cewa shiryawar karya yayi da gwamnan Jihar, Fayose
7. Kungiyar Boko haram ta saki wani sabon Bidiyo
Kungiyar Boko Haram ta saki wani sabon Bidiyo a jiya inda take gargadin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ta sha alwashin kai hari a fadar shugaban kasa
8. DSS baza ta iya sakin Zakzaky ba saboda yaji rauni
Ana cewa DSS na cigaba da tsare Sheik Ibrahim Zakzaky ne saboda yan wani rauni da sojojin Najeriya suka ji mashi a lokacin da suke kokarin kama shi a lokacin da akayi rikici a Zariya
9. Kakakin majalisar Edo yaki sauka
Bayan gwagwarmayar kokarin cire shi da aka sha, kakakin majalisar ya rantsar da wani sabon dan majalisar ta jihar
10. Naira na cigaba da kara karfin
A wanan makon, bincike daha Naij.com ya nuna cewa Dala 1 na kamawa Naira 318-320
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.