Sojin kasa sun murkushe sansanin masu garkuwa da mutane (hotuna)
– Sojojin Najeriya suke ci gaba da aikin kula inda sun kama wasu masu laifi
– An bayyana wanda Dakarun sojin kasa sun tarwatsa sansanin masu garkuwa da mutane
– Wannan ta auku a wata jihar a Kudu maso gabashin Najeriya
Jaridar Rariya ta rahoto wanda, Dakarun 14 Brigade Garrison dake yankin Ohafia, a Lahadi 10, ga watan Afirilu, sun yi nasarar gano wani sansanin masu garkuwa da mutane a garin Nkporo dake karamar hukumar Ohafia a jihar Abia.
A yayin farautar, sojojin sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi a garin Aba a ranar 6 ga watan nan, wanda har ta kai ga masu garkuwar sun harbe shi. Haka kuma an kama daya daga cikin masu garkuwar, mai suna Mista Chidiebere Sunday, yayin da kuma ragowar mutane biyun suka gudu. Wani daga cikin membobin masu garkuwar kuma, a yayin da ya fasa rufin kwanon gidan a lokacin da yake kokarin guduwa, ya fado daga saman rufin inda ya fado da ka, wanda a dalilin haka ya mutu.
KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS take so kisan gila akan Inyamirai
Sojojin sun kuma gano bindigu a wurin masu garkuwar kamar haka, AK-47 rifles guda biyu, AK-47 rifle magazine guda tara, makare da harsashai, Pistol daya da harshashai a ciki da kuma kudi naira milyan biyar da dubu dari hudu da casa’in (N5,490,000.00).
Sauran kayayyakin da aka gano a wurin su sun hada mota kirar Toyota RAV4 jeep mai lambar rijista; MUS 428 RZ, kakin sojoji, wayoyi guda shida, katin cire kudi (ATM) da kuma tabar wiwi.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin rundunar sojojin, Kanal Sani Kukasheka Usman.
Ga hotunan a kasa:
Wani mai garkuwa da mutane wanda soji sun kama
Kudaden da yawa da wayoyi kuma wadanda an karbo
Bindigogi daban daban
A wajen gidan masu laifi
Babbar gado acikin daki
Akwai iri irin abubuwa cikin daki
Cikin
A wajen sansansin masu garkuwa da mutane
The post Sojin kasa sun murkushe sansanin masu garkuwa da mutane (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.