Hotunan Saukar shugaba Muhammadu Buhari a kasar China
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu isa kasar China inda ake sanya rai zayayi kwanaki a kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari
A cewar wata takardar manema labarai da jami’i mai hudda da jama’a na shugaban kasa Buhari, Femi Adesina, shugaba Buhari da isar shi ya samu tarba daga Mr Cheng, wanda shina mai taimaka ma Ministan harkokin waje na kasar ta China.
KU KARANTA: Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata
Shugaba Buhari kuma ya samu tarba da daga; Gwamna Ajimobi na Oyo, Gwamna Amosun na Ogun, da gwamna Geidam na Yobe.
Ana sanya rai shugaban kasa Buhari zaya cinma yarjejeniya da gwamnatin kasar China domin taimaka ma Najeriya a fannin Sufuri, Noma, da kuma wutar lantarki.
Shugaban kasa Buhari kafin tafiyar, ya bayyana ma Xinhua, Kamfanin Dillacin Labaran kasar China, cewa, Najeriya bazatayi wasa da damar data samu daga wurin kasar China ba.
Shugaban kasa Buhari dai shine shugaban kasar Afirika na farko wanda shugaban kasar China, Xi Jinping, ya gayyata tun bayan da aka karkare taron Afirika da China a Johannesburg, Afrika ta Kudu.
Idan za’a iya tunawa, gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhmmadu Buhari yana yin amfani da kudaden al’umma yana tafiye tafiye marassa amfani. Gwamman ya shawarci Buhari zaya zauna domin ya fiddo da hanyoyin da za’a iya gyara Najeriya.
Haka zalika jam’iyyar LP ta hanyar Abdulkadi Abdulsalam ta shawarci Buhari daya kafa kwamitin mashawarta akan tattalin arziki. Sun bayyana cewa ana bukatar kwararru domin a cinma wannan muradi.
A wani labarin kuma, shugaba Buhari bai sanya ma kasafin kudin shekarar 2016 hannun ba. Wannan yazo ne bayan da gwamnatin take zargin yan majalisa da cirewa ko kuma kara wasu aiyuka a cikin kasafin kudin na 2016.
The post Hotunan Saukar shugaba Muhammadu Buhari a kasar China appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.