Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata 11 ga watan Afrillu, ku duba domin ku same su.
Manyan labaran da suka fice a ranar Talata 11 ga watan Afrillu
1. Wa’adin kwanakin barazana sun kare
Wa’adin kwanakin da Fasto Chrish yaba gwamna Elrufai sun cika. Faston ya nemi Elrufai daya canja dokar wa’azi daya sanya a jihar ko ya fuskanci hushin ubangiji
2. An binne tsohon gwamna Alameiyesiegha
An binne tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Alameiyeseigha bayan daya hade zuciya a lokacin da hukumar EFCC tayi kokarin kama shi.
3. Fasto TB Joshua ya bayyana wani mummunan abu zaya sami Najeriya
Babban Faston cocin SCON, TB Joshua, ya bayyana cewa wani mummunan abu na shirin samuwar Najeriya
4. Shugaba Buhari ya tafi kasar China ziyarar kwanaki 4
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar China, inda ake sanya rai za yayi kwanaki 4 a can.
5. Wahalar Mai da ake fuskanta, gwamnati ta saki Mai ga yan kasuwa
Gwamnati ta bayyana cewa ta saki Mai zuwa ga yan kasuwa domin a saukake wahalar Mai da ake fama da ita a tarayyar Najeriya.
6. Kungiyar MASSOB ta sanya takunkumi ga Nwodo, Wogu
Kungiyar MASSOB ta sanya takunkumi ga tsohon gwamnan Enugu, Nwodo, da kuma tsohon Ministan kwadago, Wogu, da kada su sake shiga kasar Biafra
7. Shugaba Buhari ya ziyarci kasashe 22 tun hawan shi mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasashe 22 tunda aka rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu na 2015. Zuwa lokacin da zaya dawo daga China, shugaban kasan yayi kimanin awanni 249 a cikin sararin samaniya.
8. Shugaba Buhari ya isa kasar China
Shugaban kasa Buhari ya isa kasar China inda ake tsammanin zasu tattauna da shugaba Xi Jinping na China akan taimaka ma Najeriya.
9. Daliban jami’ar Fatakwal sunyi zanga zanga akan kara kudin makaranta
Daliban jami’ar Fatakwal sunyi zanga zanga akan kara kudaden makarantar. Sun kulle hanyoyin shiga da fita na makarantar.
10. An damke wani wanda ya saki hotunan saduwa da mata 42
An damke wani matashi dan shekara 22 bayan ya saki hotunan wasu yan mata masu yawa dayi lalata dasu.
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.