Dakarun sojoji sun kashe yan ta’adda da yawa, sun kama kwamandoji 3 (hotuna)
– Dakarun daga sojojin Najeriya da Kamaru sun mamaye boyewar yan kungiyar Boko Haram
– Sojin sun harbe yan ta’addan Boko Haram inda guda 22 sun mutu
– Dakarun kuma ceto mutane wadanda aka garkuwa da su guda 1,275 daga yan ta’addan
An ji wanda an kama manyan kwamandoji daga kungiyar Boko Haram
Kimanin mutane wadanda aka garkuwa da su guda 1,275 daga yan ta’addan Boko Haram, sun samu yanci saboda kokarin sojojin Najeriya da Dakarun a karkashin Multinational Joint Task Force (MNJTF) daga kasar Kamaru.
KU KARANTA KUMA: Soji sun kama masu garkuwa da mutane
Rahotanni na nuna cewa wanda sojojin Najeriya da Kamaru sun kashe yan Boko Hartam guda 22, inda sun kama kwamandoji guda uku, inda Dakarun sun kai farma akan boyewar wadanda aka zargin yan ta’addan Boko Haram a gafe iyakar Najeriya da Kamaru.
An bayyana hakan acikin takardar daga Kanal Sani Kukasheka Usman, wani mukaddashin Daraktar sojojin kasa akan jama’a da hudda, wanda ya aika ma jaridar NAIJ.com.
Wani soja da tutar yan kungiyar boko Haram
Soji sun hallaka sansanin yan ta’addan Boko Haram da wutar
Mutane wadanda aka garkuwa da su
Wani tutar yan ta’addan
Dakarun inda suka rushe tutar yan Boko Haram
Sojoji masu kokari da motocin yaki
Inda Dakarun suka kone sansanin yan Boko Haram
Ana hallaka sansanin yan ta’adda da wutar
Dakarun sojoji da tutar Boko Haram
The post Dakarun sojoji sun kashe yan ta’adda da yawa, sun kama kwamandoji 3 (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.