An bayyana akan yan bunburutu a jihar Kaduna
– Malam Nasir El-Rufai gwamnan jihar Kaduna yake yi kokari da gyra matsaloli wadanda suke fuskanta jihar
– An bayyana wanda Rainin Hankalin da yan bunburutu suka yi wa yan sanda a jihar Kaduna
Wani dan jarida mai suna Ibrahim Ammani ya ruwaito daga jihar Kaduna wanda, tun bayan dokar haramta sana’ar bunburutu da gwamnatin Nasiru El-Rufa’i ta yi, sai ya zamana wata kasuwar bayan fage ta budu ga yan sanda a fadin jihar, inda ‘yan sandan ke farautar yan bunburutu ruwa a jallo, da kuma yin awan gaba da jarkokin man fetur dinsu.
Lokacin da ‘yan bunburutun suka kara fahimtar cin zarafi da ‘yan sandan suke yi musu, bayan sun kora su sai su yi gaba da jarkokin su na mai, su biya bukatun kansu da kansu, hakan ya sanya wasu ‘yan bunburutun shirya wa ‘ yan sandan gadar zare.
KU KARANTA KUMA: Buhari na samu karbuwa na tenuwa na biyu
Lamarin ya faru ne a wani gidan mai dake Command Junction Unguwar Sabo Kaduna, inda ‘yan bunburutun suka ciccika jarkokinsu da ruwa, sannan suka tara su wuri guda kamar fetur, suna zaune sai ga ‘yan sanda masu sintiri sun iso wajen, suna ganinsu sai ‘yan bunburutun suka arce da gudu, su kuma ‘yan sanda suna isowa ba su yi wata -wata ba, sai suka kwashe jarkokin man suka loda a motocinsu, sannan suka bude daya daga cikin jarkokin man, suka cika tankin motarsu, a dai-dai wannan lokaci ne suka fahimci ruwan rijiya ne ba man fetur ba, su kuma ‘yan bunburutu a gefe guda suka yi ta musu dariya.
Malam Nasir El-Rufai, wani gwamnan jihar Kaduna
Wasu mutane wadanda sun rubuto akan shafin Facebook na jaridar Rariya sun bayyana tunaninsu akan hakan. Na farko, Suhail Saliss yace wanda, ai ba manyan yan bunburutu kamar masu gidan mai da suke saidawa akan 220 per liter suyakamata akama bamasu galanba xalincine
Na biyu, akwai Hashim Saidu kuma yace, gaskiya mu wannan anyi yanda zamu dinga sham wahala ne kawai.. Bamu da cigaban da za ahana musu bumburutu..da ace akwai fetur a kowani gidan mai, da babu wanda zai siya a wurin ‘yan bumburutu.. kuma gaskiya anshiga haqqin wasu saboda wasu daga cikinsu suna da mata da yara har da iyaye.. idan aka hanasu sana ar to meza suci har subiyama yaransu karatu.. Gaskiya dai yakamata a dubi wannan hukuncin
Na uku, Anas Hoja gsky nima ina ganin ba yan bunburutu ya dace a dinga kamawa ba masu gidajen mai dake sayarwa 250 ya dace akama wahala. Na hudu, Auwal Abubakar Agaskiya yakamata gwbnati tacilastawa masu gidan mai subudae ko suhadu da hushin hukuma akoina cikin kasarnan
Na biyar Sufyan Masu’dWallahi kunyi dai dai xalintarku akaso ayi ai badan akwai yan bunburutun ba wahalar man xaifi saboda ana samu awajensu dan an hanasu baxaisa abawa masu abin hawa ba tunda ai masu gidan man sune cikakkun yan bunburutu.
The post An bayyana akan yan bunburutu a jihar Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.