Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis 21 ga watan Afrillu. Ku duba domin ku same su.
Saraki a CCT
1. Alkalin kotu CCT ya bada umurni a kama Lauyan Saraki
Mai Shari’a Danladi Umar, ya bada umurni a kama lauyan Saraki, Raphael Oluyede akan rashin biyayya ga kotun
2. Amurka zata sanya hoton wata bakar fata akan kudin ta
Harriet Tubman itace mutum ta farko, bakar fada wanda za’a fara saka hoton ta akan kudin Amurka
3. Yan kunar bakin wake guda 2 sun tada Bam.
Yan kunar Bakin wake guda 2 sun tada Bam a sansanin yan gudun hijira inda suka hallaka mutane 8.
4. Yadda Shekau ya taimaki yan Shia
Mallam Baba Ahmad na nbabban zauren musulunci ya bayyana cewa kungiyar Shia tafi ta Boko haram hadari ga Najeriya.
5. An cire Ministan Mai a matsayin shugaban kamfanin NNPC
Hukumar kula da kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya bayyana cewa labarin karya ne cewa an kori Ibe kachikwu a matsayin shugaban kamfanin.
6. Dan Ibrahim Babangida ya maganta akan lafiyar baban shi
Dan tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya maganta akan lafiyar baban shi.
7. Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jakadan Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jakadan Amurka ta majlisar dinkin duniya, Samantha Power
8. Saraki ya nemi Alkali Umar ya cire kanshi daga Shari’ar shi
Shugaban majalisar Dattawa ya nemi Alkalin Danladi Umar na kotun CCT daya fidda kanshi daga shari’ar da yake yima shugaban majalisar akan cewa hukumar EFCC na bincikar shi.
9. NFF ta nada sabon Cocin Najeriya
Shuiabu Amodu shine sabon cocin kungiyar Kwallon kafa ta Najeriya
10. Shugaba Buhari ya gana da Andrew Forest
Shugaban Buhari ya gana da shugaban kungiyar Walk free domin tabbatar da yancin Bil adama.
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.