Nasarar mu na nan kusa – Kungiyar IPOB
– Kungiyar IPOB ta bayyana cewa tana godiya ga dukkan mabiyar kungiyar akan jajircewa da kwazon da suka nuna
– Kungiyar ta bayyana cewa nasara na nan kusa babu jimawa
– Ta bayyana cewa kiran da tayi ya ja hankalin mutane da yawa
Magoya bayan kungiyar Biafra
Kungiyar mutanen Biafra ta IPOB, a jiya Alhamis 21 ga watan Afrillu, ta bayyana cewa nasara na nan kusa kuma babu gudu babu ja da baya.
KU KARANTA: Femi Falana zaya kai Fulani makiyaya kotun duniya
Kungiyar ta bayyana cewa jan hankalin mutane datayi akan abubuwan dake faruwa ya ja hankalin mutane da yawa fiye da yadda sukayi tsammani. Jaridar The Sun ta ruwaito.
Dakta Clifford Iroanya tare da Emma Mmezu, jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar ne suka bada wannan zance inda suka saki takarda ga manema labaru.
Suka ce ” Duk da yadda muke da makiya wadanda suke so sun hana mu, wannan gamgami namu ya samu goyon baya, taimaka, jajircewa daga mutanen da bamu mayi tsammani ba.
” Jajricewar ku, tsimmar ku ta ja hankalin duniya inda a yanzu kowa da kowa ya san kuna gwagwarmaya kuma kuna tsoratar da abokan gaba.
” Muna yi maku godiya ta musamman , ina alfahari daku.
“Muna kuma godiya ga dubunnan magoya bayan mu daga Jihohin Kogi, Kwara, Benue, Cross Rivers akan jajircewar sa sukayi. Wannan ya isa kurma ya ji, makaho ya gani, kuma azzalimi ya ruga a cikin rudani ya rasa inda zaya sanya kanshi.
” Da farko sun fara zargin mu da kashe Hausa-Fulani guda 5. Daga baya sai suka dauki hayar wani mutum da babu shi, wai Babalola Samson. Kirkiri duniya taga wawancin su a fili.
Idan za’a iya tunawa, a 1966 ne aka fara yin juyin mulki a Najeriya. Wanda wannan ya jawo mutuwar manyan mutane daga Arewacin Najeriya, inda kuma dan kabilar Igbo, Aguyi Ironsi ya amshi shugabancin kasa. Daga baya ne sojojin Arewa suka ture shi inda Ojukwu shi kuma ya ja aka fara yakin Basasa.
The post Nasarar mu na nan kusa – Kungiyar IPOB appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.