Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июнь
2016

Mummunan ambaliyar ruwa ya afka ma garin Abakalki

0

Wani mummunan ambaliyar ruwa ta afka ma garin Abakalki dake jihar Ebonyi. Kamar yadda shaidu suka ambata ambaliyar ruwa ta faru ne sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka yi tun daga ranar asabar har zuwa ranar lahadi.

Ambaliyar Ebonyi

Mazauna garin da yawa ne dai musamman na kusa da ruwa suka rasa gida jen su sannan kuma wasu da yawa iska ya kware masu rufin gidan su sakamakon ruwa da iskan da akayi. Wuraren da abun ya fi shafa dai sun hada da Ogbaga Road, Udensi Street, St. Patrick Road, Hill Top, Mile 50, Nkaliki, Ogbe Hausa, Ogoja Road da dai sauransu.

KU KARANTA: Shugabannin kungiyar Ibo sunyi kira ga Buhari

Haka ma dai wasu coci-coci dake a bakin ruwa duk abun ya shafe su. Wasu masu shaguna ma dai a titin Ogboaga da gidajen dake a Hilltop Avenue duk ambaliyar ta shafesu. Wani daga cikin wadan da abun ya shafa Mr. John Oke ya shaida ma manema labarai cewar ambaliyar ta tafiyar masa da komai nashi hadda takardun sa masu muhimmanci sosai.

A cewar sa: “kawai mun tashi da safe ne sai muka gan mu cikin ruwa tsundum don saida ma na sha wahara kafin in iya fidda yara na waje”.

The post Mummunan ambaliyar ruwa ya afka ma garin Abakalki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *