Naira ta dara Dala a kasuwar bayan fage
Naira ta yi rawar gani a kasuwar canji a ranar Litinin 13 ga watan Yuni, an sayar da Dala a kan N355 daga N362 a ranar Juma’a 10 ga wata
Naira Dubu daya
Darajar kudin Najeriya Naira ta hau da Naira 7 tsakanin ranakun Juma’a zuwa Litinin. Sai dai Nairar ta yi kasa a kan fam na Ingila a inda ake sayenta a N510 da kuma Yuro a inda ake sayenta a N405.
KU KARANTA: Ana kai hare hare a Nija Delta saboda Jonathan ya fadi
Sai dai farashin gwamnati na Dala ya kasance N197 a babban bankin kasar. Masu saye da sayarwa a kasuwar canjin na cewa an samu wadatar kudin musayar ne.
Wani mai sana’ar canji a Legas ya shaidawa NAIJ.COM cewa “An samu ci gaba saboda yadda Dalar ke dan kewayawa a hannun jama’a. Mu na kuma fatan hakan ya ci gaba”.
NAIJ.COM na iya tuna cewa alamun da ke bayyana cewa an boye kudaden kasashen waje na sayarwa ne, bayan da wani kwamitin na babban bankin kasar mai kula da tsare-tsaren kudi ya sanar da cewa za’ a bar Naira ta samowa kanta daraja a kasuwar canji.
Hawa da saukar darajar Naira ya dogara ne a kan bukatar kudaden na waje, da kuma yawaitarsa a hannun jama’a. Za ku iya sanin yadda farashin kudaden kasashen waje suke a shafin NAIJ.COM
The post Naira ta dara Dala a kasuwar bayan fage appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
