Hare haren neja delta saboda faduwar Jonathan ne- Senata
– Sanata Adamu Aliyu yace ‘yan bindigan neja delta na cika alkawuran su na fusata gwamnatin Najreriya
– Yana rokon ‘yan Najeriya da su taimaka wa Buhari domin yakan masu son raba kan kasa
– Ya ce ‘yan bindigan na kai har hare ne domin an kada jonathan a zabe
Tsageran Nija Delta
Senata Abdullahi adamu ya bayyana cewan dililin da yasa ‘yan bindigan neja delta ke kai hare hare kafufuwan man kasa a yankin neja delta kawai domin a lashe jonathan a zaben ne. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe tsohon shugaban kasan ne a shekarar 2015,wanda ya kafa tarihin farko na kada shugaban kasa mai ci.
KU KARANTA: Jihohin Rivers da Bayelsa zasu fuskanci karancin Mai
Tsageru neja deltan sun dau alhakin kai hare hare na tashin bam ga bututun mai a yankin , abin ya karu ne ma duk da janye sojojin da gwamnati tayi daga yankin. Jaridar daily trust ta bada rahoton cewa ,Senata Abdullahi Adamu da ke wakiltar mazabar nasarawa ta yamma a majilisar dattawa ya bayyana hakane a lakcan watan ramadanan da jami’ar jihar nasarawa ta shirya a keffi.
Senatan Yana mika kokon baransa ga ‘yan najeriya da su taimaka wa buhari domin yakan masu son raba kan kasa.
Ya ce;
“Masu gudanar da wadannan ayykan dama sun sha alwashin yin hakan idan tsohon shugaban kasa bai lashe zabe ba saboda dan uwansu ne, sun fadin hakan kuma jaridu da kafafen watsa labarai da dama sun bayyanar da hakan.
“Yan Najeriya ba zasu yi nadamar zaban shugaba buhari ba , kuma a matsayina na dan majalisar dattawa na kasa,ina fada muku cewa gwamnati na sassauci ne kawai saboda hakkin marasa alhaki.”
Hakazalika, wani ‘mai himmar aiki dan yankin ta neja delta, Ankio Briggs ya bayyana cewa tsagerun neja delta ba ‘yan najeriya bane, daga Somalia suka zo. Mr. Briggs wanda dan hannun daman jonathan za fadi hakan ne a wata taruwan shekara na kungiyar matasan ibo wato ‘igbo youth movement’ ta shirya. Briggs yayi Allah tirr ya ayyukan tsagerun kuma ya jaddada cewan ‘yan Somalia ne, ba yan Najeriya ba.
The post Hare haren neja delta saboda faduwar Jonathan ne- Senata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.