Jihohin ribas da bayelsa zasu fuskanci wahalan man fetur
– Da rabon jihar ribas da bayelsa su fuskanci man fetur
– Kungiyar NUPENG ta umurce gidajen mai da su kulle gidanjen man su kuma su shiga yajin aikin da ta keyi
– A yanzu haka ,Kungiyar NUPENG na yajin aikin saboda kamfanonin mai guda hudu da suka ki bin manufofin su
NNPC
Jihohin ribas da bayelsa zasu fuskanci wahala da rashin man fetur a bisa ga umurni da kungiyar gamayyar ma’aikatan man fetur da gas na kasa wato NUPENG ta ba gidajen man da ke jihohi biyun da su kulle gidajen mai,kuma su shiga yajin aiki.
KU KARANTA: Barazanar kungiyar Nija Delta Avengers
NUPENG a yanzu suna yajin aikine saboda kamfanonin mai guda hudu da suka ki bin manufofin su. Kamfanonin man sune , Hilong Engineering Limited,Uniterm Nigeria Limited,Specialis Dilling Fliud Limited,and Fudro Nigeria Limited.
Game da rahoton jaridar Punch, Shugaban kungiyar ta yankin fatakwal, Mr Charles Eleto, yace babu gidan man da za’a daka wa kafa, duk gidan man ta ki kulle wa sai an cita tara.
“ A bisa da yajin aikin da NUPENG ke kai, ana umurtan duka gidajen mai da su ma suka shiga yajin aikin.
“Na san wasu gidajen basu shiga ba tukun,shi yasa muke bada umurnin yanzu ,in kunne yaji,gangan jiki ta tsira.
“Ma’aikatan matatan ma fetur sun shiga,direbobin tankokin mai sun shiga, gidajen ijiyan mai masu zaman kansu sun shiga,domin haka ya zama wajibi gidajen mai su shiga,” ya fada”
Ya mika kokon baran sa zuwa ga gwamnonin jihohin guda biyu da kuma jami’an tsaro da su tabbatar da cewa kamfanonin guda 4 sun daina zalunta ma’aikatan su.
“Ba wanda zai mana barazana,innama zamuyi amfani da abun da muke dashi mu samu abinda muke so. Kamfanonin man sune , Hilong Engineering Limited,Uniterm Nigeria Limited,Specialis Dilling Fliud Limited,and Fudro Nigeria Limited.
“idan ‘yan najeriya sun kuntata, suyi kira da kamfanonin ta bi dokokin mu domin cima manufofin da na jama’a, saboda abubuwan da suke yi ya saba wa ka’idojin kowani kungiyar ‘yan kwadago. Shi yasa muka fara da jihoyin ribas da bayelsa” Eleto,yayi gargadin cewa fa su baza su dawo daga yajin aikin ba sai kamfanonin guda 4 ta shirya sulhu.
The post Jihohin ribas da bayelsa zasu fuskanci wahalan man fetur appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.