Kungiyar Niger Delta Avenger daga Somalia-Ms Briggs
-Ms Briggs ya soki ayyukan yan kungiyar Niger Delta Avengers da Fulani makiyaya a kasar
-Ta ce mayakan ba daga Najeriya suke ba amma akwai yihuwa daga Somalia
-Alex Ekueme wadda yake a taron yayi kira ga jumhuriya na gaskiya
Tsagerun Nija Delta
Ankio Briggs, mai himmar aiki daga yankin Niger Delta, ta yi da’awar cewa tsagerun Niger Delta Avengers ba daga Najeria suke ba, amma daga kasar Somalia.
Kungiyar ta dauki alhakin jerin harin bom daga man petir, da kuma bututun gas a yankin, sun kuma sha alwashin ci gaba da yin haka har sai dukkan gurin samar da mai na yankin ya ginu.
NAN sun ba da rahoton cewa, Ms Briggs wacce ke kusa da dan kuran tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta yi Magana a gurin al’ada na kungiyar Igbo Youth Movement da suke yi shekara-shekara, zama na 17,tare da taken “Najeriya”, har yanzu suna bi akan gaskiyar kasafin kudin jumhuriyya
Ms Briggs tayi Allah wadai da ayyukan yan bindiga, ta kuma nace akan cewa basu kasance daga yankin Niger Delta ba amma daga Somalia.Ta kuma soki kisan wata Bridget Agbamihe, da wasu yan zanga-zanga sukayi a jihar Kano akan aikata sabo, da kuma Fulani makiyaya a wasu sassa na kasar.
KU KARANTA KUMA: An saka bam a Obi Obi Brass Truck Line
Alex Ekueme, wanda shine tsohon mataimakin kasar, yayi kira ga sake fasalin al’amura na kasar a matsayin yadda mulkin mallaka suka shirya, cewa ko wani yanki yayi aiki da mulkin kai.
Jerry Gana wadda yake tsohon ministan bayanai, ya shawarci gwamnati da tayi aiki na gaskiya a jumhuriya. “ Kasafin kudin jumhuriyya na gaskiya ne kawai zasu ba da daman zaman lafiya, da kwanciyar hankali a kasar, kuma a bar ko wani yanki su sarrafa albarkatun su ta hanyar da suke so.”
wani shugaban kabilar Yoruba, Ayo Adebanjo, ya bayyana cewa yawan rikicin siyasa a kasar ya samu ne saboda ba’a tsara mulkin kasar yadda ya kamata ba. A taron, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya goyi bayan sake fasalin al’amuran kasar kan kasafin kudin jumhuriyya, amma ya yi gargadi ya yin da yake jawabi, akwai bukatar magance yawan kudin shugabanci cikin gaggawa. Duk wani gwamna da yace bazai iya biyan ma’aikata albashi ba, Obi yace, ya kamata ya ba da hanya ga sauran mutane mafi alheri
The post Kungiyar Niger Delta Avenger daga Somalia-Ms Briggs appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.