Kotu ta kora dan majalisar wakilan PDP ta kasa
– Babban kotun tarraya ta kora ‘dan majalisan tarayya dan jam’iyyar PDP mai wakiltan mazabar udi/ezeagu ta jihar enugu, Dennis Amadi
– Kotun tace zaben firamaren jam’iyyar PDP da Amadi ya ci bogi ce
Ofishin jam’iyyar PDP
Wata babbar kotun tarayya da ke zauna a Abuja ta kora ‘dan majalisan tarayya mai wakiltan mazabar udi/ezeagu ta jihar enugu, Dennis Amadi. A shari’ar da aka gudanar a ranar juma’a 10 ga yuni,Alkali mai shari’an Okon Abang yace zaben firamaren da Amadi yaci anyi ba bisa ga doka ba kuma domin haka bogi ce.
KU KARANTA: NECA ta nemi taimakon Sifeton Yan sanda
Abang yace amma yaben jam’iyyar PDP ta gudanar a ranar 6 ga disamba 2014,halaliya ce. Kuma ya sake tabbatar da cewan Ogbuefi Ozomgbachi ne ya lashe zaben firamaren.
A bisa ga shari’ar, Abang ya umurci hukumar gudanar da yabe ta kasa wato INEC da ta ba wa Ozomgbachi shahadar cin zaben da gaggawa kuma ta kwace wanda ta bawa Amadi,kuma shi amadi ya bar majalisa kai tsaye.
Alkalin kotu mai shari’ar Yace;
“Bayan kyakkyawan dubi ga karar da aka kawo,na tabbatar da cewan zaben da aka gudanar a mazabar udi/ezeagu ta jihar Enugu a gaban ma’aikatan INEC a ranar 6 ga disamba da gaske ne , na ga cewan mai karar ne ya lashe zaben a bisa ga cika ka’idojin jam’iyyar.
“Dennis Amadi kuwa, ya dawo da duk kudanden da ya karba a matsayin albashi,alawus, da duk abin da ya karba tun ranar da ya shiga majalisa” Ya kara. Abang kuma yace mai amsa kara na farko ya bawa mai karar naira 100,000.
The post Kotu ta kora dan majalisar wakilan PDP ta kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.