Na so motoci suyi aiki da gas a Najeriya- Obasanjo ya yi magana
-Obasanjo ya ce ya yi nufin motoci suyi aiki da gas lokacin da yake kan mulki
-Tsohon shugaban kasa ya ce ci gaban iskar gas a Najeriya na daga cikin shirin sa
-Ya bayyana cewa, ya ba da lasisi ga kamfanoni a kokarin ganin cewa ya cimma wannan burin
Buhari da Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana haka a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, a lokacin wata ziyara da hukumar Nipco Plc yayi gare shi a fadar shi na Abe0kuta, jihar Ogun.
Ya ce yayi nufin motoci suyi aiki da iskar gas domin rage dogaro akan shigo da man petir.
Obasanjo ya ce ya bayar da lasisi ga kamfanoni a kokarin ganin cewa ya cimma wannan kudurin, kari da cewa, da yanzu kaso 50 na motoci a kasar na aiki da gas. A shekarar 2006, gwamnatin Obasanjo ya bayar da lisisi ga kamfanoni uku, Nipco Plc, Contact Global da kuma Global Steel, don ci gaban iskar gas ga motoci.
Amma an hada cewa Nipco, wanda ya hade da kamfanin Nigeria Gas Company don samar da Green Gas Limited, ya kashe muhimmanci a cikin aikin tun sa’a nan. A cewar shi, a birnin Benin, jihar Edo, sama da motoci 4,000 ne suka yi aiki da CNG wanda ke haifar da gurbinlita miliyan 20 na man petir daga shekara ta 2012 zuwa 2015 kuma da tanadin fiye da $9m.
Shugaban ya bayyana cewa, a duniya, a duniya babu fiye da biliyan 150 cubic metre na Associated Gas (AG) walkiya a ko wace shekara, Afrika na walkiyan kimanin cubic metre biliyan 40 a ko wani shekara
The post Na so motoci suyi aiki da gas a Najeriya- Obasanjo ya yi magana appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
