To fa: rabuwar kai tsakanin yan bindigan neja delta
– Kan ‘yan bindigan neja delta ta rabu a bisa zaman sulhun da ake shiryawa da gwamnatin tarayya
– A yayinda wasu bangaren na son a yi, wasu sun ce sam
Jaridar vanguard ta bada rahoton cewa an samu rabuwar kai tsakanin yan bindigan neja deltan da ke kai hare hare kafufuwan man kasa dake yankin ta neja delta kwanakin nan. Wannan ya faru ne a dalilin da shelar da wadansu wai ‘shiryayyun matasan egbesun neja delta sukayi.
KU KARANTA: Ya’yan shugaba Buhari sun halarci taron Mahaifiyar su
Da yawa daga cikin yan bindigan sun fusata ne cewan su kawai ana amfanin dasu ne domin cimma wata manufa daban . Kungiyar shiryayyun matasan egbesun neja delta na hayaniya da kunigiyar ta tsagerun neja delta ne.
Kungiyar ta dau mazauna daya da kungiyar gamayyar kwato yancin neja delta wato JNDLF akan a tsagaita tsegumin, kuma ta nuna banbancin ra’ayinta game da maganar sakin nnamdi kanu da sambo dasuki. JNDLF ta ita ta amince da tayin zaman sulhun da gwamnati takeyi. Amma Kungiyar tsagerun neja delta fa ta ce sam, bata a cikin wani sulhu. Masu gudanarda shirye shiryen sulhun na gwamnati sun fara ganawa da wadansu yan bindigan kuma ba da dadewa ba , zasu tsagaita wuta a kuma zauna da gwamnati.
The post To fa: rabuwar kai tsakanin yan bindigan neja delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
