Saraffa tattalin arziki, Babangida ya gaya ma Buhari
Tsohon gwamnan jihar Niger, Alhaji Babangida Aliyu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sarrafa tattalin arziki
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci sarrafa tattalin arziki kuma, domin kawar da wahalar da yan Najeriya. Tsohon gwamnan jihar Niger, Alhaji Babangida Aliyu yayi wannan kira a ranar Lahadi a garin Abuja, a lokacin wata hira da kamfanin New Agency of Najeriya (NAN).
“Tsawon shekaru masu yawa mun kasance muna Magana game da sarrafa tatalin arzikinmu, amma mun ci gaba da dogaro akan man petir.
“Yanzu da farashin mai ya rushe kuma wahala ya zo, muna bukatar sarrafawa yanzu, muna bukatan tattaunawa, amincewa, da kuma aiwatar da azumi akan tattalin arziki.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya sake jerin sunayen jakadai
“ A’a karda mu bar mutane a cikin duhu da tunanin cewa wannan gwamnatin ta sa wannan, cewa gwamnati ce ta janyo haka.”
Babangida Aliyu ya ce:“Ina ganin ya kamata mu dubi cewa, mun yi kuskure na tsawon shekaru masu yawa kan dogaro ga tattali arziki kuda daya kan man petir kuma yanzu ne lokaci da ya kamata mu sarrafa.”
Ya yi kira ga Musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na Ramadan gurin yin addu’a ga kasar, su taimaka wa mabukata da kuma canji gurin ganin ci gaban kasa. A halin yanzu, yan Najeriya na cikin mawuyacin hali yayin da bankin koli, Central Bank of Nigeria (CBN) ta iyakance yawan kudin da za’a iya cirewa kan N10,000, bi ga manyan kudi da ke ajiye a asusun abokan ciniki.
The post Saraffa tattalin arziki, Babangida ya gaya ma Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.