Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июнь
2016

Labari da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan karar Buhari

0

A sakamakon shigar da bukatar janye karar da Nnamdi Nwokcha – Ahaaiwe ya kai Muhammadu Buhari na a rashin cancanta, Kotun ta soke karar.

A wani da labari da jaridar Cable ta bayar ta ce, mai shari’a Adeniyi Ademola na babban kotun tarayya ne ya yanke hukuncin korar karar, a ranar Laraba 30 ga watan Yuni a Abuja,

Shugaba Muhammadu Buhari

KU KARANTA: Kungiyar CAN sun kai hari ga Shugaba Buhari

A cewar mai shari’ar a yayin yanke hukuncin, “A bisa Sashe na 50 (2) na tsarin dokokin babbar kotun tarayya, na soke wannan kara”. A baya dai mai shari’a Ademola ya daga karar ne har iya wani lokacin da bai bayyana ba.

A cewar mai shari’ar ya daga sauraron shari’ar ne saboda sanarwar da Buhari ya ba kotun na daukaka kara. A ranar 15 ga watan Yuni ne Buhari ya daukaka kara bisa hukuncin kotun na watsi da rashin ammanarsa ga karar da Nwokocha ya yi.

KU KARANTA: Ido- da ido: Ana cacar baki tsakanin Buhari da Saraki

Wanda ya shigar da karar, Nnamdi Nwokocha na kalubalantar sahihancin takaradun shaidar karatun shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, a inda ya ke zargin shugaban da rashin cancantar tsayawa takarar zabe a tun farko, saboda a cewarsa, shugaban ba shi da mafi karancin shidar ilimi da zai halasta masa shiga takarar zabe.

Rahotanni na cewa Nwokocha ya janye karar ne salin-alin, bayan zargin da ya yi na cewa a na yin barazana ga rayuwarsa sakamakon shigar da karar.          

The post Labari da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan karar Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *