“Dalilin da ya sa na ke kwana da gawa”
-Wani dan kasar Ghana ya furta cewa ya na kwana da gawawaki a wani shirin talbijin a kasar
-Mutumin ya ce aikin da ya ke yi ne sa mata suka guje shi
Wani mutum mai suna Lucas Shakar dan kasar Ghana ya furta cewa ya na kwana da gawa, ya na kuma na biyan bukatarsa da gawawwakin mata matattu a irin da ya ke yi.
Lucas ya ce ya kwanta da gawawwakin mata daban-daban
A hirar da mutumin ya yi da gidan talbijin na Adom TV na kasar, mutumin ya bayyana yadda ya ke tarawa da gwawwakin mata daban-daban a yayin aikinsa.
Lucas wanda ma’aikacin dakin ajiyar gawa ne na wani asibiti a kasar, ya kuma bayyana dalilin sa na tarawa da mata matattu da cewa, mata masu rai sun ki shi, saboda aikin da ya ke yi na kula da gawwaki. Ya na mai cewa “Ina son in yi aure amma ‘yan mata guduna suke yi, saboda ni mai kula da gawwaki ne, don haka na ke biyan bukata ta da gawwakin mata matattu”.
KU KARANTA: Wata Yar Najeriya ta janyo tashin tashina a Indiya
A cewar sa kwanciya da gawar mace ya samo asali ne daga horon da ya samu a lokacin da za’a dauke shi aiki asibitin koyarwa na Korle Bu da ke Ghana, domin a cewarsa, “Idan ka yi lalata da gawa, to ka daina jin tsoron kowacce irin gawa kuma”.
Mai gabatar da shirin ya tambaye shi anya kan sa daya? Sai Lucas ya amsa masa da cewa lafiyarsa kalau. Sai dai gama yada shirin ke da wuya, asibitin da ya ke aiki suka sallame shi.
The post “Dalilin da ya sa na ke kwana da gawa” appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.