Yan gargajiya sunyi Magana akan rikicin hijabi na jihar Osun
-Yan gargajiya sun mayar da martani kan rikicin hijabi na jihar Osun
-Yan gargajiya sun bukaci gwamnan jihar, Rauf Aregbesola ya zama tsaka tsaki kuma sun nemi cewa karda a bayyana jin zuciyan addini a makarantu
Yan gargajiya sun maida martani a kan rikicin hijabi a jihar Osun. Yan gargajiya da dama da sukayi Magana da jaridar Punch, sunce makaranta ba gurin shiga ta addini bane. Aregbesola wadda ya kasance mattataran rikicin addini a jihar, kan amfani da Hijabi da dalibai musulmai sukeyi a makarantun gwamnati, ya ce gwamnatin sa bazata daure da haka ba. Channesl tv ta ruwaito.
Yan gargajiya sun bukaci gwamnan jihar, Rauf Aregbesola ya zama tsaka tsaki kuma sun nemi cewa karda a bayyana jin zuciyan addini a makarantu
Sun bukaci gwamnatin jihar da ya zo da shiga daya, ba tare da jin zuciyan wani addini ba.
KU KARANTA KUMA: FIRS ta rufe kamfanoni kan kin biyan kudin haraji
Chief Olatunji Bamidele, mai bautan Ifa, yace: “Abunda ya kamata gwamnatin jihar tayi shine ta zamo tsaka tsaki, ba wai ya ta karkata ga gefen dama ko hagu ba. Wannan ita ce hanya mafi dacewa gurin magance matsalar. A bangaren Idowu Esuleke, babban bokan Esu, jihar Osun, ya ce , matsalar ba wai na gwamnan ko kungiyar CAN bane. Gwamnatin ya samu shiga daya da dukkan makarantu zasu dunga yi. Haka zalika, Adedoyin Talabi Olosunfaniyi, yar rukon Susan Wenger tace idan dalibai suka koma gida zasu iya sa ko wani irin kaya da suke so.
The post Yan gargajiya sunyi Magana akan rikicin hijabi na jihar Osun appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.