kungiyar IPOB sunyi Allah wadai da Niger Delta Avengers
-Babban majalisar IPOB sun bayyana cewa basu da kawance da kungiyar Niger Delta Avengers
-Dattawan sunyi Allah wadai da tashin hankalin da kungiyar MASSOB keyi, da kuma rahoto da akayi na cewa suna kawance da yan’bindiga
-Sun kuma bukaci yan’Najeriya suyi hakuri cewa za’aji dadi nan gaba
Babban majalisar dattawan Indigeneous People Of Biafra (IPOB) sun fitar da abokanta na pro-Biafra,wato kungiyar Movement for the Actualisation of the Sovereign State of Biafra, da kuma kungiyar Niger Delta Avengers don barazanar da sukeyi ga zaman lafiya a kasar.
Kungiyar guda biyu sun yi da’awar amincewa da ayyukan juna kuma sun sha al’washin taimakawa junansu dan ganin sun cimma bukatar su.
KU KARANTA KUMA:Sojoji sun kashe yan kungiyar Boko Haram
Jaridar The Punch ta rahoto cewa, babban majlisar IPOB sunyi Allah wadai da ayyukan su kuma sunce akwai alamu da ke nuni da cewan basu shaida yakin Biafra ba.
Dr. Dozie Ikedife wanda shine shugaban babban majalisar a Nnewi, jihar Anambra, a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, ya bayyana cewa, da’awar da akeyi cewa wasu daga cikin yan kungiyar pro-Biafra suna aiki da kungiyar Niger Delta Avengers da wasu kungiyar yan’bindiga ba gaskiya bane, cewa irin wannan alaka bazai haifar da abu mai kyau ba.
Ya ce ya shaida yadda aka yan-yanka miliyoyin mutanan Igbo a lokacin yakin basasa, dan haka bazai goyi bayan ko wani tashin hankali ba. Yace za’a iya dawo da dukiyoyin da aka rasa amma baza’a iya dawo da wanda ya mutu ba.
The post kungiyar IPOB sunyi Allah wadai da Niger Delta Avengers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.