An kona wani mutum kurmus a Jihar Delta
-Hotuna sun fara yaduwa na hukuncin da wasu mutane suka yankema wani mutum
-Mutumin yayi ma wata yarinya fyade ne na fitan hankali
-Mutanen cikin fushi,suka banka masa wuta har lahira
Wani abun takaici ya faru a Unguwar Ekuigbo dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta a ranar laraba 29 ga watan yuni, yayinda yan unguwa suka banka wa mutum wuta, sai dai ya tashi a lahira.
inda aka banka ma wani wuta
Abun zargin na cikin yan daban da yi ma wata yarinya yar kasuwakuma yar shekara 22 mai sayar da abincin kifi fyade ,a ranar litinin 27 ga watan yuni.
Jaridar daily post ta bada rahoton cewa kakakin hafsan yan sanda,Mr. Celestine Kalu, ya tabbatar da labarin, yace an fara gudanar da bincike akan al’amarin. Mr. Celestine yace budurwar na jinya a asibitin central da ke Jihar.
Daga baya munyi iyakan kokarin sake ganawa da kakakin yan sanda domin samun cikon labarin amma bamu samu daman ganawa da shi ba.
KU KARANTA: Labari da dumi duminsa: Ojo Maduekwe ya Rasu
Amma mun samu daga majiya da dama cewa yarinyar ta mutu daga baya, sai mutane suka je farautar wadanda suka yi fyaden, suka kama guda 1 ,suka masa kunan gashin masara zagaye da masu kallo har hafsoshin yan sanda.
The post An kona wani mutum kurmus a Jihar Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.