Har yanzu dai ba hujjan sata akan Buratai
Yan Najeriya daga kowani sassa suna tofa albarkacin bakin su a cikin zancen cewa Gwamnatin tarayya ta wanke shugaban jami’an sojin kasa na kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai akan kadarorinshi na kasan waje.
An tuhumce Buratai da mallakan kadarori a kasar Dubai da kudin kwangilan sayen motocin da Gwamnati ta bada. Gidan Jaridar Sahara Reporters ce ta bayyana cewa shugaban jami’an Sojin kasa na kasan ya mallaki wasu dukiya a kasar Dubai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban hafsin sojin Najeriya mai suna Laftanat Janar Tukur Buratai
Zargin cewan kudin kwagilan motocin ya taso ne yayinda sojoji da hafsoshi, musamma yan yankin Arewa maso gabashin kasar suka yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa ayi bincike cikin kwangilan motocin. Labarin kwangilan ne yasa yan Najeriya suka yi kira da hukumomin yaki da rashawa suyi binciken Tukur Buratai.
Saboda wadannan maganganun, gwamnatin tarayya, a ranar talata,28 ga watan yuni, ta saki wani jawabin cewa ta kamala bincike akan shugaban jami’an sojin kasa na kasan kuma ta wanke shi daga zargin da ake masa , ta ce kadarorin da mallaka;ya mallake su ne da zufan shi. Game da Jawabin :“ Gwamnatin tarayya,bayan gudanar da binciken da tayi akan labaru da yaduwa a kafafun yada labara na cewan Janar Buratai ya mallaki dukiya a Dubai, mun gano cewan shi da iyalenshi sun saya hannun jari ne kamar yadda kowa zai iya saya. Zaku iya gudanar da taku binciken akan haka.”
KU KARANTA : Janar Buratai yayi magana game da zargin da ake masa
Yan najeriya kuwa, sun yi Allah wadai da bayanin da gwamnatin tayi akan al’amarin . sunce yunkurin wanke Buratai ci baya ne ga yaki da rashawan da Shugaba Buhari keyi. Wasu sunce buratai yayi murabus da gaggawa kuma ya sallama kanshi domin bincike.
Haka zalika ,buratai yace yan kungiyan boko haram ne ke gindin labarun kadarorinsa na Dubai.
The post Har yanzu dai ba hujjan sata akan Buratai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.