Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июнь
2016

An fidda Enyimba daga gasar zakarun nahiyar Afirika

0

Kulob din Enyimba ya sha kashi a hannun kulob din Mamelodi Sundowns na South Africa da ci 2 – 1 wanda hakan ne ya fitar da ita daga gasar zakarun na Afrika.

Mai tsare ragar Eyimba

Kulob din na South Africa ya samu nasarar fara cefa kwallo a zango na farko na wasan ta hannun Leonardo Castro a cikin minti na 42. Daga bisani ne kuma Oluwadamilare Ojo na Enyimba ya zura tashi shima a cikin minti na 59.

Masu masaukin bakin na South Africa sun samu damar zura kwallon tasu ta hannun Arendse. Kulob din na Enyimna dai ya zuwa yanzu ya rasa wasanni biyu kenan a jere.

Mai karatu zai iya tunawa cewa a baya kulob din na Enyimba ya sha kashi a hannun kulob din Zamalek na kasar Egypt a garin Port Harcourt da ci 0 – 1.

The post An fidda Enyimba daga gasar zakarun nahiyar Afirika appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *