Rabaran Mbaka na yi wa Buhari addu’a
–Rabaran Mbaka ya na zargin wasu ‘yan Najeriya da kokari shiga tsakaninsu da shugaban kasa
-Limanin kiristan ta karyata zargin cewa ya hangowa Buhari gaza warkewa daga larurar da ya ke fama da ita
Limanin darikar Kotolikan mai yawan janyo cece-ku-ce, Rabaran fada Ejike Mbaka, ya bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya na kokarin shiga tsakanin cocinsa Adoration Ministry da ke Enugu da gwamnatin Muhammadu Buhari.
Fr. Mbaka da Buhari a yayin wata ziyara da ya kai masa bayan zabe
Malamin cocin da ake ganin kamar ya yi amai ne ya lashe ne, ya ce, ba kamar yadda kafofin yada labaran kasar ke watsawa na cewa shugaba Buhari ba zai samu waraka daga rashin lafiyar da ta ke damunsa ba, ba haka ba ne.
KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan karar Buhari
Mbaka ya ce likitocin Najeriya ne suka nuna shakkun su na warkewar shugaban, kuma ya maimaita abinda suka fada ne, amma ba furucin sa ba ne. A maimakon haka ma shi addu’a ya ke yi wa Buhari a na samu lafiya.
A wata sanarwa da limamin cocin ya fitar a ranar 30 ga watan Yuni, ta hannun jam’insa mai hulda da jama’a, Cif Barr Maximus Ugwuokwe, sanarwar ta karyata zargin da ake cewa limanin Cocin ya furta wadannan kalamai, sannan sanarwar ta ci gaba da cewa, “…sun ce duk larurar da ta shafi kunne, ta shafi hanci da kuma wuya, don haka muke ta addu’a ga shugaban kasa ya samu lafiya, shi da duk wadanda ke fama da irin wannan larura mai hadari”.
Rabaran Mbaka na daya daga cikin ‘yan kalilan da suka hangowa Buhari nasara a babban zaben shugaban kasa a shekarar da ta wuce, wanda hakan ya sa ya shiga tsaka mai wuya a waccan lokaci.
The post Rabaran Mbaka na yi wa Buhari addu’a appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.