Olisa Metuh na son mayar da Naira miliyan 400 – Lauyan sa
Cif Olisa Metuh ya bayyanar da dalilin da yasa yake son mayar ma Gwamnatin Tarayya Naira miliyan 400 da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan y ba shi. Da yake Magana ta hannun Lauyan sa, Onyechi Ikpeazu (SAN) Mista Metuh ya ce bai san daga in da kudaden suka fito.
Olisa Metuh a Kotu
Cif Olisa Metuh ya bayyanar da dalilin da yasa yake son mayar ma Gwamnatin Tarayya Naira miliyan 400 da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan y ba shi. Da yake Magana ta hannun Lauyan sa, Onyechi Ikpeazu (SAN) Mista Metuh ya ce bai san daga in da kudaden suka fito.
Ya ce “ Wanda nake wakilta bai san daga inda kudaden suka fiti ba, hakan ya tabbata a yanzu daga hujjojin da mai kara ya baje ma Kotu da kuma batutuwan shaidu. Wanda muke wakilta yana da yakinin cewa kudin sun fito ne daga wurin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da ya bada umarnin a sakan masa bayan ya zayyan mai bukatan haka, kuma na bayar da rohoton duk abin da aka yi da kudin”
“lokacin da lamarin ta taso kuma aka gayyaci Cif Metuh zuwa ofishin mai bai da Shawara na kasa (ONSA) a watan Disamba na 2015, ya bukaci ya san daga ina kudin ya fito, kuma ya yi bayyana niyyar sa na mayar da kudin idan daga Asusun Gwamnati suka fito, da tare da la’akarin cewa na kashe kudaden kamar yadda tsohon Shugaba ya bada umarni”
Ma’aikatan Ofishin mai bada shawara akan tsaro na Kasa basu kara waiwayar sa ba kamar yadda suka alkarwanta, har sai lokacin da EFCC ta damke shi a watan Janairun bana. “har said a aka je Kotu ne da aka kawo wata takardar da ke nuni ga inda kudaden suka fito, kuma tun daga sannan wanda muke wakilta ya kara bayyana niyyar sa na mayar da Kudin, sa’annan ya tunkari danginsa, yan’uwa da abokan arziki da su taimaka su harhada mai Kudin da zai don ya mayar da dukkan Naira miliyan 400 zuwa ga baitul malin Gwamnati ba tare da la’akarin cewa an kashe kudaden kamar yadda tsohon Shugaban Kasa yayi umarni, kuma an samu wasu daga cikin kudaden daga shaidun mai kara”
Lauyoyin Metuh sun fada cewa azal ce kawai ta hau Sakataren watsa labarai na PDP, tsautayi ne kawai. “Yunkunrin sa na mayar da kudaden na nuni ga irin goyon bayan da yake bayar wa akan yaki da rashawa, kuma hakan na nuni ga dattakunsa da gaskiyar sa a kan al’amarin.” Ya kara da cewa “Babu shakka mun lura masu kara sun fara kashe kudade a wannan shari’ar, fatan mu ne ba zasu rage ko sisi ba daga kudin da aka mayar zuwa yanzu, da haka, ba za’a cimma muhimmin manufar dawo da kudade ba.
The post Olisa Metuh na son mayar da Naira miliyan 400 – Lauyan sa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.