Fayose yana takular Buhari
-Wa’adin da mai dakin shugaban kasa taba Fayose ya kare ranar 29 Yuni.
-Amma Fayose bai janye zargin da yayi ma mai dakin Buharin ba.
-Matar Buhari ta bar kasar yau zuwa Saudi Arabia domin yin umra.
Fayose da Aisha Buhari
Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, A’isha Buhari ta ba gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose kwanaki biyar ko kuma ya fuskanci shari’a. Matar shugaban kasar ta rubuta ma gwamna Ayo Fayose takardar gargadi tana bukatar shi da ya janye zargin.
Fayose ya zargi Buhari in da yake mai cewa Buhari ba waliyyi bane, ya kuma zargi matarsa da hannu a cikin abin kunyar nan na cin hanci da rashawa da ake kira Halliburton scandal.
KU KARANTA : An kama mai-tsaron Buhari da alaka da Bokoharam
Cikin takardar da lawyoyin ta suka rubutake mai suna “bukatar ka janye zargin da kayi na karya wanda jaridu da yawa suka buga ranar 20 Yuni 2016 a kan wadda muke wakilta mai girma matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mrs. A’isha Buhari”.
The post Fayose yana takular Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
