Rikicin yin Jabun Dokoki: Bita da kulli ake mana-Majalisar Dattijai
Majalisar Dattijai ta mai da martini dangane da zancen da aka ce Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal yayi in da yake cewa ai ba Majalisar dattijan ke Kotu ba a karar da Ministan Shari’a na kasa ya shigar da Shugaban majalisar Dattijai da mataimakinsa. A dayan hannun kuma Majalisar t ace ai ba’a ambaci sunan Saraki da Ekwaranmadu ba a karar.
Sakataren ya bayyan haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 29 ga watan Yuni, inda ya ce ba wai sabon abu bane a shigar da karar wani akan lafin yin jabun dokoki, ya kara da cewa ai an taba shigar da tsohon kakakin majalisa na Kasa Salisu Buhari a kan mallakan Jabun shaidar kammal Makaranta, wanda hakan ne yayi dalilin murabus din da yayi.
Sai dai mai Magana da yawun Majalisr, Sanata Aliyu Sahabi Abdullahi ya ce Majalisar Dattijai bata gamsu da matsayin da Sakataren ya dauka ba, kuma ta doge akan matsayinta, ya ce “Majalisar Dattijai ce ake yi wa bita da kulli, it ace ake so a tsoratar domin a tursasa musu sabon Shugabanci” ya kara “ya kamata Mista Babachir Lawal ya fada mana idan ana tuhumar Shugaban Kasa da mataimakinsa akan laifin da ka iya sa su rasa kujerun su, ba Gwamnatin Buhari ake hari ba? ”
“Ya zama dole mu shaida ma mutane cewa, ba kamar maganr da Sakataren Gwamnati yayi ba, Lauya mai kara bai ambaci sunan Shugaban majalisa Saraki ba, ko na mataimakin sa Ekweranmadu ba, haka kuma wadanda Yansanda suka yi hura da su a yayin binciken basu ambaci sunan Shuwagabannin majalisar ba, haka ma a cikin rohoton Yansanda”
“Bari mu tuna Mista Lawal hakikanin shari’ar da aka yi a 1999 na tsohon Kakakin majalisa. A bayyane yake ba’a tuhumar Shugaban majalisa ko mataimakin sa da amfani da jabun shaidun kammala makaranta kamar yadda aka tuhumi tsohon Kakaki Salisu Buhari. Don haka, kada ma a fara kamanta su. Bugu da kari, shekarun Saraki da Ekweranmadu ba su yi kadan na su rike mukaman da su kai ba, kamar yadda yake a cikin Tuhumar Salisu Buhari ”
Duk wani yunkuri kamanta lamrukan guda biyu, yunkuri ne kawai na maayar da yan Najeriya Jahilai wadanda ba su san tarihi ba. Ya na cewa “Muna sane da cewa babu yanda za’ayi a tuhumci wani da rubuta sa-hannun sa na jabu. Ba hurumin sashin Zartarwa bane ta san dokokin majalisa na gaskiya. Har zuwa 29 ga watanYunin shekara 2015, ranar da aka rantsar da Majalisar Dattijai, Shugaban majalisa da mataimakin sa Sanatoci ne kamara kowane Sanata, saboda haka ba su ma da ikon canja dokokin.”
“A matsayin ta na Mjalisar Dattijai, da kuma na Majalisar dokokin Kasar nan, ta yi bayyan fahimtar ta game da cin mutuncin da sashin zartarwa ke yi ma yancin cin gashin kan su. Fahimtar mu itace an shirya wannan shari’ar ce don a kawo cikas ga al’amuran shugabancin majalisar Dattijan, a canja shugabancin ta kuma a mallake yan majalisun”
“A ganin masu hannu a cikin wannan bita da kullin, Shari’ar nan ta fiye musu muhimmanci ba wa a tsaya a magance dimbin matsalolin da ke damun Kasar nan ba, Duk da haka, muna da yakinin ba za su samu nasara ba. Fatan mu kadai shi ne su sakan ma Sashin shari’a mara ta gudanar da ayyukanta kuma ta yanke Shari’a akan radin kan ta.
The post Rikicin yin Jabun Dokoki: Bita da kulli ake mana-Majalisar Dattijai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.