Kotun zabe ta tabbatar da nasarar David Mark
-Wata kotun zabe ta tabbatar da Senata David Mark a matsayin senatan da ke wakiltar mazaban benuwe ta kudu.
-Kotun zaben tayi watsi da takardar karar da dan jam’iyyar APC,Daniel Onjeh,ya gabatar akan zaben
onjeh da mark
Wata kotun zabe da ke zaune a makurdi,babban birnin Jihar Benuwe ta tabbatar da zaben tsohon shugaban Majalisan dattawa,Senata David Mark.
KU KARANTA : Kotu ta yanke hukunci kan karar Buhari
A yau ne, ranar alhamis,30 ga watan yuni,kotun zaben tayi watsi da takardan karan da dan takarar senata mazaban Benue ta kudu karkashin jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar ranar 20 ga watan Febrairu,Daniel Onjeh, ya mika ma kotun. Akan kara ne, Alkalin Kotun, Jastis Dipeolu , ya tabbatar da zaben a watan oktoba . Amma Daniel Onjeh bai amince da shari’ar ba, za kai kotun daukaka kara wacce ta yanke hukuncin rusa zaben kuma tace a sake.
An sake wata sabuwar zaben bayan kotun daukaka kara ta rusa waccan a ranar 28 ga watan maris,2015 wadda hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar da cewa David Mark ya lashe zaben. Duk da hakan, an sake wata zaben a ranar 20 ga watan Febrairu kuma David Mark ya sake lashe zaben. Onjeh bai daddara ba, ya sake koma kotu ya kai karar rashin amincewar sa da zaben, ya fada ma kotun ma ta shellanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Senata David Mark yay i kira ga kotun da ta yi watsi da takardar karar Daniel Onjeh saboda ta wuce kwana 21 da dokar kasa ya zantar.
The post Kotun zabe ta tabbatar da nasarar David Mark appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.