Dan kunan bakin waken Boko Haram ya kasha Mutum 11
-Wani dan Kungiyar Boko Haram ya kai hari wata kauye a kasar kamaru kusa da bodan Najeriya
-Gwamnan garin yace a yanzu mutane 11 ne suka mutu,ya na kira ga mazauna garin da su bi dokar gwamnati.
Wani gwamnan kasar Kamaru ya bayyana cewa harin kunan bakin waken da wani dan kungiyar Boko Haram ya kai ta kasha mutane 11, da kuma masu raunuka iri iri. Gwamnan garin yayi kira ga masu farin hula su bi a hankali,kada su karya doka wajen kokarin kare kan su daga hare hare irin wannan. Wata majiyar Jami’an tsaro ta ce dan boko haramun din ya tayar da bam din a garin Djakana kusa da boda Najeriya cikin dare. Ya ce: “Mutane 7 ne suka mutu a take a wurin, fari da dan boko haram din.”
hoton wata yar kunan bakin wake
Majiyar ta kara da cewa mafi yawancin wadanda abin ya shafa ‘yan kungiyar banga ne da ke yaki tukuru domin murkushe yan boko haram. Suna zaune a daki suna kallo,yayinda dan kunan bakin waken ya shigo,ya tayar da bam din. Ya kara
Midjiyawa Bakari,Gwamnan yankin ,ya fada wa manema labarai cewa mutane 11 ne suka mutu kuma 4 sun raunana. Ya ce: “ Hakan ya faru ne saboda rashin jin masu gidan kallo, bayan mun hana irin wadannan abubuwa, suna daukan kasada suna sa kayan kallo a cikin daji da daddare… muna kira ga jama’a da su yi hakuri su daina irin wadannan abubuwa har sai idan mun ce a cigaba, musamman a filin daga.”
Yan kungiyan boko haram suna amfani da mata da yari wajen kai harin kunan bakin wake wurare daban daban irin masallatai,kasuwanni,tashan mota,da wuraren bincikan sojoji.
KU KARANTA:Gwamnatin tarayya zata kulle Gidajen Rediyo
Bayan shugaban kasa ,Muhammadu Buhari yayi ikirarin murkushe su, sun a cigaba da halake rayukan mutane.
The post Dan kunan bakin waken Boko Haram ya kasha Mutum 11 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.